Kungiyar musulunci ta bukaci a canja dokar hana saka hijabi a makarantun horas da lauyoyi

Kungiyar musulunci ta bukaci a canja dokar hana saka hijabi a makarantun horas da lauyoyi

- Kungiyar kare hakin musulunci (MURIC) ta bukaci majalisar wakilai ta yi dokar ta zai haramta musgunawa masu saka hijabi

- Kungiyar kuma ta yi kira ga yan majalisar su tabbatar cewa babu wanda ya hana Amasa Firdausi gudanar da aikin ta a matsayin lauya

- Kungiyar ta sake jadada cewa amfani da hijabi wajibi a addinin Musulunci

Direktan kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola ya aike da wasika ga shugaban kwamitin Shari'ah na Majalisar Wakilan Tarayya inda ya bukaci 'yan majalisar suyi garambawul ga dokar sanya tufafi a makarantun horas da aikin lauyoyi a kasar nan.

Kungiyar musulunci ta bukaci a canja dokar hana saka hijabi a makaratar horar lauya
Kungiyar musulunci ta bukaci a canja dokar hana saka hijabi a makaratar horar lauya

A rahoton da jaridar Leadership ta ruwaito, Kungiyar kuma ta bukaci a hukunta malamar makarantar horas da lauyoyin da ta cire hijabin Amasa Firdausi kuma ta taka shi a kasa domin wannan cin mutunci ne ga musulunci.

KU KARANTA: PDP ta mutu a Jihar Legas, an kuma binne ta - Jam'iyyar APC

Wasikar kuma ta ce badakalar na hijabin Firdausi Amasa ya sa an gano babbar matsala da matan musulmi suka dade suna fuskanta a wuraren aiki da makarantu daban-daban a fadin kasar nan misali wuraren samun fasfo na tafiya kasashen waje, wajen karban lasisin tuki, wajen neman katin zabe da sauransu.

Kungiyar ta jadada cewa saka hijabi wajabi ne ga mata musulmi, bugu da kari kundin tsarin mulkin Najeriya ya bawa kowa damar ya gudanar da addinin sa ba tare da tsangwama ba da kuma daraja hakin dan adam.

Daga karshe, Kungiyar ta yi kira ga majalisar na wakilai ta tashi tsaye wajen ganin cewa an kwato ma Firdausi Amasa hakkin ta kuma a tabbata babu wanda zai hana ta gudanar da aikin ta a matsayin lauya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164