Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017

Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017

Kamar dai a kowace Majalisar Tarayya a duniya, ta Najeriya ma ba ta tsira daga hayaniya, hayagaga, cece-ku-ce, harkalla kai har ma da bahallatsa a 2017 ba.

Legit.ng ta samu damar kawo muku wasu bakwai da su ka fi saura yin kaurin suna a gurugubji da yamutsa gashin-baki walau a majalisar ne, mazabun su da Jihohin su.

1. DINO MELAYE

Shi ne Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, kusan ya fi saura shiga tsomomuwa da kuma yin taratsi a 2017. Tun a cikin Maris hayaniya ta tirnike ilahirin kasar nan a kan zargin cewa Melaye ya kantara karyar kammala Jami’ar A.B.U Zaria.

Bayan wannan, Melaye ya sake shiga rikicin da ya sake yin kaurin suna, bayan da ‘yan mazabar sa 188,580 su ka rattaba hannun bukatar a yi masa kiranye.

A zaman yanzu wannan shari’a na kotu inda ta ke tafiyar hawainiya bayan da Dino ya garzaya kotu ya kai INEC wacce ke da alhaki da ikon yi masa kiranye.

Sai kuma cikin Oktoba, inda aka nuno wani hoton sa tare da wata matar da ba a san kowa ce ba. Shi ma wannan ya haifar masa da tsugune-tashi.

Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017
Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017

2. BUKOLA SARAKI:

Bukola Saraki dai a cikin 2017 ya zama – shari’a ba ta sa gaban ka ya fadi. Kuma ya ya zama kura kun saba durkuso gaban alkali.

Katan-katanar Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa ta samo asali ne daga tuhumar da CCT ta dade ta na yi masa, amma aka kori karar, ko kuma a ce kotun ta wanke shi cikin watan Yuni.

Amma kuma sai murna ta koma ciki a cikin watan Disamba, yayin da Kotun Daukaka Kara ta sake maida Saraki Kotun CCT domin ya amsa wasu tuhumomi 18 da ake zargin sa.

3. SHEHU SANI:

Kusan Sanata Shehu Sani ya shafe 2017 ya na rikici da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Shehu da El-Rufai dai su biyun duk baubawan burmi ne – yayin da El-Rufai ke ganin cewa babu gwani sai shi, Shehu Sani kuma na yi wa El-Rufai kallon duk abin da ya yi ba daidai ba ne.

Ya zargi El-Rufai da tinjima jihar Kaduna cikin rijiyar bashi mai gaba dubu, wacce Allah kadai ya san shekarar da za a iya tsamo jihar daga ciki.

Baya ga alamomin da ya nuna cewa zai tsaya zaben 2019, ya fito ya soki lamirin tsayawar da El-Rufai ke neman sake yi a zaben 2019.

Cikin Satumba kuma ya ragargaji APCin Kaduna da ta amince El-Rufai ya sake tsayawa, ya na mai cewa, “APCin Kaduna ta sake jibga wa al’umar jihar dagwalon masana’antu.”

Shehu ya kuma caccaki gwamnan bayan ya kori malaman makaranta sama da 20,000.

Shi dai gwamnan ya ce Shehu ya sa kafar wando daya da shi ne, don ya ki nada ko da mutum daya daga cikin mutanen da Shehu ya turo ya na so a nada kwamishinoni.

Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017
Waiwaye adon tafiya: Sanatoci 5 da gangar su tafi amo a 2017

4. ISA MISAU:

Sanata Isa Misau daga Bauchi, ya daura banten kokawa da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris, run daga ranar da ya zargi Shugaban ‘Yan sandan da yi masa karya wajen bada rahoton dalilin da ya sa Sanatan ya yi ritaya daga aikin dan sanda.

Daga nan shi ma sai ya zargi Sufeto Janar din da yin aure a asirce tare da wata jami’ar ‘yar sanda da ya ce hakan ya karya dokar aikin dan sanda.

Wannan rikici ya sa kwamitin Majalisar Dattawa ya sa gayyatar sufeton amma ba ya halarta. A ranar da ya je, ya shaida musu cewa shi ba abin da zai ce, domin magana ta na kotu.

5. ALI NDUME:

Sanata Ali Ndume ya hadu da fushin Majalisar Dattawa a lokacin da ya nemi a binciki Bukola Saraki da Dino Melaye a kan zargin da wasu jaridu su ka ce Dino ya yi fojare. Shi kuma Saraki bi-ta-da-kulli ya ke yi wa Shugaban Hukumar Kwastan, ba cika-aiki ba.

An dakatar da Ndume wata shida. Bayan cikar wa’adin, an yi kokarin kara masa wasu yawan kwanaki, amma ya garzaya kotu, kuma ya yi nasarar cewa hatta waccan dakatarwa da aka yi masa haramtacciya ce, don haka sai a biya shi dukkan albashi da alawus-alawus na watannin shida.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng