Sarakunan gargajiya da aka yi a Zazzau, Amina ta nawa ce?
A waiwayen mu na tarihi na yau, zaku ji jerin sunayen sarakunan Fulani da aka yi a Zaria cikin shekaru 200 da doriya da suka wuce, zaku san ko Sarauniya Amina ta nawa ce
Birnin Zazzau dai yana daga cikin garuruwan Hausa Bakwai wadanda a labari ake cewa Bayajidda ko Bawo, ya kafa a kasar Hausa. Wanda ya aika 'ya'yayensa na halak. Banza bakwai kuma kamar su Nupe da Kebbi, ya aika 'ya'yayensa shegu, domin su mulka.
An kafa birnin Zazzau ne a shekarar 1536, miladiyya, a wani yanki na dausayi, kudu da hamada, maraya ce da ta hada manoma da malumma da masu kasuwanci.
Sarkin Farko a wancan lokaci sunansa Gunguma.dan Bawo. Bawo kuwa a Hausance shine Bayajidda na Sarauniya Daurama.
Zaria ita ce kanwa ga Amina shine kuma sunan da ta baiwa babban birnin Zazzau, kusa da dutsen Kufaina, a karni na 16 ne aka sanya wa Zazzau wannan suna. Sarauniya Zariya ta gaji Amina wadda rasu a 1610 m. a garin Attagara, bayan da ta ci Kano da Katsina da yaki. Ita ma kuma ta rasu a Yawuri, bayan gajeren mulki.
Fadin iyakar inda ta ci da yaki ya kai daga jihar Filato ta yanzu a gabas, zuwa Abuja da kewaye, kamar su Nupe da Nassarawa. A arewa kuma har Daura da Katsina ta hadiyo. Ta kuma shafe shekaru 30 tana mulki.
Mahaifiyarsu ita ce Bakuwa Turunku, ta 22 a jerin sarakunan Zazzau, kafin zuwan fulani. Ita ta kafa garin Turunku, kudu da Zazzau, a kan hanyarta ta yake-yake da kabilun Nupawa da Gwarawa.
Kafin dai fulani su ci Zariya da yaki, a 1807ca, anyi sarakuna 60 Hausawa 'yan asalin garin da yankin, watau sarakunan Habe, wadanda wasunsu sun bi addinan gargajiya, wasunsu kuma suka yi musulunci.
Sarki Jatau dai a tarihi, wanda yayi mulki daga 1742-1802 shi ya fara musulunta ya kuma gina masallaci na farko. Bayan rasuwarsa, dansa Makau, ya koma addinin gargajiya, ya kuma rushe masallacin.
DUBA WANNAN: An kama shugabar NSITF ta lokacin Jonathan
Sai dai a 1804, da Usmanu dan Fodiyo ya fara jihadi, Malam Musa, malami kuma bafillace, ya je Gobir ya karbo tuta daga Shehu, inda ya hada karfi da Yamusa, bafillacen Borno, suka kawo wa Makau yaki.
Makau ya tsere zuwa Zuba, inda Abuja take a yanzu, inda ya rayu da kabilun yankin kuma a nan ya rasu. Su kuwa su Malam Musa suka tabbatar da abin da mahaifinsa ya faro, watau Masallaci da addinin Islama.
Malam Musa shine Sarkin Fulani na Farko, kuma ya rasu a 1821, sai Yamusa ya amshi mulki, inda yayi mulki har 1834. Daga nan sai Malam Abdulkarim, bakatsinen bafillace, kuma dalibi ga Malam Musa ya karbi mulki. Kuma daga wadannan gidaje ne har yau, ake samar da sarakunan Zariya.
1. Mallam Musa (gidan Mallawa) 1804-1821
2. Yamusa (gidan Barnawa) 1821-1834
3. Abdulkarim (gidan Katsinawa) 1834-1846
4. Hamadu dan Yamusa 1846
5. Muhamman Sani dan Yamusa 1846-1860
6. Sidi Abdulkadir dan Malam Musa 1860 (ture shi aka yi)
7. Abdussalami (sullubawa) 1860-1863
8. Abdullahi dan Hamadu dan Yamusa 1863-1873 (an ture shi) sai a 1876-1881 (aka sake ture shi)
9. Abubakar dan Malam Musa 1873-1876
l0. Sambo dan Abdulkarim ( gidan Katsinawa) 1881-1890 (shima tumbuke shi aka yi)
l1. Yero dan Abdullahi dan Hamadu 1890-1897
i2. Kwasau dan Yero 1897-1902 (tumbuke shi aka yi)
Zuwan Turawa
13. Aliyu dan sidi Abdulkadir 1902-1923 (shima an tumbuke shi)
14. Dallatu dan Yero 1923-1924
15. Ibrahim dan Kwasau 1924-1936
16. Malam Ja'afar dan Ishaq 1936-1959
17. Alamin dan Usman 1959-1975
18. Shehu Idris 1975-har yau.
Turawa sun iso da rundunoni na yaki har biyu, a 1900 domin mulkin mallaka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng