Wani hisabin sai a Lahira: Direba ya yi ma budurwa fyaɗe, sa’annan ya shaƙe mata wuya har ta mutu
Wani asararren mutumi dake aiki da wata makarantar koyar da tukin Mota, Lizzu Driving School dake garin Abekuta na jihar Ogun mai suna Festus Udo ya hallaka wata budurwa yar bautan kasa.
Kwamishinan Yansandan jihar, Ahmed Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Laraba 14 ga watan Disamba yayin da ya jagoranci yan jaridu zuwa inda Udo ya yi ma budurwar mai suna Modupe Taiyesi fyade da karfin tuwo, daga bisani kuma ya kashe ta, inda aka tarar da gawar ta fara rubewa.
KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige jigo a kungiyar Miyetti Allah saboda ya fallasa su
Premium Times ta ruwaito kwamishina Iliyasu yana fadin Udo ya yaudari Modupe ne da karyar zai koya mata tuki, sa’annan ya samar mata izinin tuki, don haka ne ta yi rajista da makarantar koyon tuki.
Shugaban hukumar bautan kasa, NYSC, ta jihar Ogun John Okon ne ya fara shaida ma kwamishinan cewa wata daga cikin masu yi masa kasa hidima a jihar ta bace, daga nan ne Yansanda suka fara bin diddigi.
“Binciken mu ya kai mu ga wani mai suna Fetus Udoh, wanda ke koya ma Madupe tuki, da haka ne har muka kai ga kama shi, tare da gano inda ya bar gawar budurwar. Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, bayan Udo ya kira ta, tazo su yi tuki, shi ne ya kai ta har zuwa wannan daji.” Inji kwamishinan.
Shi ma wanda ake tuhumar ya shaida ma yan jaridue cewa “Bayan na kai ta zuwa dajin, sai na fada mata ina so in yi amfani da ita, amma ta ki, ni kuma sai na ja ta da karfin tuwo zuwa dajin nan, kuma na zakke mata, bayan na gama ne, sai ta ce sai ta fada ma yan uwanta, ni kuma sai na yaga rigar ta, na shake mata wuya da shi.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng