Ku sadu da wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

Ku sadu da wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

Wani mutum mai suna William Masvinu dan asalin kasar Zimbabwe ya sake lashe kambun wanda yafi kowa muni a karo na biyar a cikin karshen satin da ya gabata a yayin wani gagarumin taro da aka gudanar a can kasar dake cikin Afrika.

Shi dai William ya yi rashin sa'a a shekarar da ta gabata ne inda wani wanda ake kira Maison Sere ya kada shi a cikin wata gasar mai cike da sarkakkiya.

Ku sadu da wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5
Ku sadu da wanda ya lashe kyautar mafi muni a duniya karo na 5

KU KARANTA: Saura kiris inyi murabusa a shekarar 2016 - Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa a wannan karon dai kuma sai shi William din ya sake shiri inda ya lashe kyautar ya kuma samu kyautar kudin da suka kai dala dari 500 yayin da shi kuma wanda ya zo na biyu aka bashi dala dari 200.

Da yake zantawa da manema labarai kuma, Masvinu ya bayyana matukar jin dadin sa da ya lashe gasar a wannan karon inda kuma ya godewa dangin sa da mahaifan sa da ma dukkan masoyan sa.

Haka ma kuma ya bayyana kudurin sa ga yadda ake so ya shiga gasar wanda yafi muni a duniya sannan ya kuma bada tabbacin cewa zai lashe kambun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng