An naɗa shugaba Buhari muhimmin Sarauta a kasar Inyamurai, kalli hotunan naɗin
A yayin ziyarar aiki na kwanaki biyu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yankin kabilar Ibo, wanda ya fara a ranar Talata, ya gamu da karramawa irin na al’adar ibo.
A jihar Ebonyi, shugaban sarakunan jihar, Eze Charles tare da sarakunansa, sun nada shugaba Buhari sarautar ‘Enyioma 1 of Ebonyi’, a harshe Hausa, Babban Abokin Ebonyi.
KU KARANTA: Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyana gaban kwamitin bincike, sanatoci sun shanya shi
Haka zalika, sarakan basu yi kasa a gwiwa ba, har sai da suka sake nada shi wani sarautar ta daban, mai taken ‘Ochioha Ndi Igbo’, shugaban al’ummar Ibo.
Legit.ng ta samo wannan rahoto ne daga shafin shugaban kasa Muhammadu Buhari dake kafar sadarwar Facebook, inda aka daura hotunan shugaba, tare da Sarakunan yayin nadin sarautar.
Shuagaba Buhari ya kai wannan ziyara ne da nufin nuna ma yan kabilar Ibo ana tare, tare da basu tabbacin cin gajiyar wasu manyan ayyuka da gwamantinsa zata gudanar a yankin.
Ga bidiyon nadin sarautar nan daga shafin Buhari Sallau:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng