Dara-ta-ci-gida: Wani dan sanda yaje sata ya baro katin shaidar sa
Wani jami'in dan sanda mai suna Williams Godwin ya jefa kan sa cikin tsomomuwa bayan da ya baro katin shaidar sa na aikin dan sanda a cikin jakar wani dan shekara 41 a duniya da yayi wa fashi da makami.
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa dan sandan ya tare mutumin ne a kan hanyar sa ta zuwa Legas daga Ibadan inda kuma ya sace masa dukkan katunan bankin sa da kuma kudaden sa Naira dubu hudu.
KU KARANTA: Buhari bayya kokarin da yayi ga inyamurai
Legit.ng dai ta samu cewa sai dai a yayin da dan sandan ke bincika jakar mutumin sai katin shaidar sa ya fada ciki shi kuma bai lura ba.
Da yake karin haske game da lamarin, Godwin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan da ya gabata na Oktoba inda kuma ta tabbatar da cewa dan sandan har kusar sa yayi da wani abu mai tsini a gefen wuyan sa.
Tuni dai jami'an 'yan sandan suka baza komar su suna neman jami'in da yanzu haka ya bi uwa duniya ya boye.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng