Ya bindige ɗansa, yayin daya kama shi turmi da taɓarya yana aikata luwaɗi

Ya bindige ɗansa, yayin daya kama shi turmi da taɓarya yana aikata luwaɗi

Wani mutumi mai suna Wendell Melton dan shekara 52 ya dankara ma dansa, mai suna Giovanni harsashi,a lokacin daya kama shi yana luwadi, inda nan take yace ga garinku a kasar Amurka.

Shi dai Giovanni mai shekaru 14 ya tsunduma cikin halin luwadi ne tun ba yanzu ba, kamar yadda tsohuwar marikiyarsa ta bayyana. Sonja Jones tace “Mahaifin Giovanni ya dade yana muzguna ma yaron.”

KU KARANTA: Kungiyar goyan bayan Buhari ta kori zargin Ndigbo akan SGF

Sai dai ta kara da cewa, mahaifin baya kaunar halin luwadi da yaron nasa ke ciki, inda hakan yayi sanadiyyar yawan samun takaddama a gidan nasu, tsakaninsa da yaron nasa.

Ya bindige ɗansa, yayin daya kama shi turmi da taɓarya yana aikata luwaɗi
Giovanni

“Na san Melton baya jin dadin halun yaron nasa, kuma na tabbata ya gwammace yaron ya mutu da a ce yana luwadi.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito Jones tana fadi.

Jone ta kara da cewa rahotannin da ta samu sun bayyana cewa mahaifin Giovanni ya shiga dakin yaron nasa a lokacin daya kama shi tare da abokinsa suna luwadin, ganin haka ya dauki bindiga ya bindige shi.

Ya bindige ɗansa, yayin daya kama shi turmi da taɓarya yana aikata luwaɗi
Uban da dansa

Amma fa a nata bangaren, matar tace bata ji dadin kisan gillar da Melto yayi ma Giovanni ba, don haka take fatan kotu ta yanke masa mummunan hukunci, kuma ta daure shi har iya rayuwarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng