Wasu kabilu 5 a tsaunin Mambila sun gudanar da taron hana barkewar rikici a yankin

Wasu kabilu 5 a tsaunin Mambila sun gudanar da taron hana barkewar rikici a yankin

- An yi taron hana barkewar sabuwar rikici tsakanin al'ummar tsaunin Mambila

- Wani kungiyar wanzar da zaman lafiya ta shirya taron

- Shugaban kwamiti na karamar hukumar ya ce rikicin da ta barke a baya ba ta da alaka da addini

Akalla kabilun tsaunin Mambila 5 ne suka taru a wani babban taron da aka gudanar a filin wasan garin Gembu domin rigakafin hana sake barkewar duk wani rikici da sunan kabilanci ko addini ko kuma kiyayya tsakanin manoma da makiyaya a yankin

An samu shirya wannan gagarumin taron ne a karkashin wata kungiya mai wanzar da zaman lafiya.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, shugaban kwamitin karamar hukumar, Pastor Godwin Sawa ya bayyana cewa rikicin da ta barke a kwanakin baya a yankin inda aka yi hasarar rayuka da dauruwan shanu da dama, ba ta da alaka da addini kuma yanzu haka an dauki duk matakan hana aukuwar irinta nan gaba.

Wasu kabilu 5 na tsaunin Mambila sun gudanar da taron hana barkewar rikici a yankin
Taron wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummar tsaunin Mambila

Shugaban ya bayyana cewa damuwar daya ce, rikici tsakanin manomi da makiyayi. Manomi yana son wurin noma haka shi ma makiyayi na bukatar wurin da zai yi kiwon dabbobinsa. Abun da ke hada fada ke nan a tsakanin.

KU KARANTA: Hukumar soji ta tabbatar da kai hari kan jami'anta a Zamfara

Babban jami’in na ‘yan sanda a yankin Sardauna, Alabura Dangi, ya ce kabilun sun zama daya domin dukansu suna fulatanci.

A zaman taron, Fulani makiyaya sun bukaci a hukumta baragurbin dake tsakaninsu da suke da hannu a kashe-kashen da aka gudanar tare da biyan diya ga wadanda suka rasa shanunsu.

Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya, Injiniya Zakari Ahmed Guroji, ya karfafa dawo da martabar sarakuna a matsayin wata hanyar hana irin wannan rikicin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng