An haifi jariri da sunan Allah rubuce a kunnuwansa a jihar Gombe
Wani abin mamaki da al'ajabi ya bayyana a jikin wani jinjiri da aka haifa a unguwar Sarankiyo dake a garin Gombe dake a Arewa maso gabashin Najeriya inda aka ga kalmar ALLAHU a rubuce da larabci a kunnuwan sa.
Maihaifin yarin dai mai suna Alhaji Hashimu Falaru shine ya fara kula da al'amarin sannan kuma ya shaidawa matar tasa kuma uwar yaron kwanaki biyar bayan haihuwar sa yayin da ya dauke sa.
KU KARANTA: Osinbajo ya caccaki shugabannin Kiristoci
Legit.ng ta samu dai cewa mahaifin yaron ya shaidawa majiyar mu ta Aminiya cewar a ranar Laraba ne dai bayan ya dauki jaririn sai ya kula da siffar kunnen sa ya yi kama da rubutun sunan Allah da larabci inda kuma ya shaidawa matar ta sa mai suna Hafsah.
Haka ma dai majiyar ta mu ta samu cewa kafin yin wannan auren nasa, Alhaji Hashimu Falalu ya shafe kimanin shekaru 15 tare da tsohuwar matar sa da suka rabu sakamakon rashin haihuwa.
An dai radawa jariri suna Muhammad Fadeel tun a ranar da aka haife shi kamar dai yadda sunna ta tanadar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng