Babban dalilin da ke sa karuwanci na karuwa a Najeriya - Malamin addini
Wani malamin addinin kirista mai suna Fasto Samuel Adegboye ya yi tir tare da tofin Allah-tsine musamman ma ga yadda yace karuwanci a tsakanin kananan yara mata a ta kara yin yawa a kasar nan ta Najeriya sannan kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta haramfa kazamar sana'ar.
Fasto Adegboye wanda kuma shine shugaban rukunin coci-coci na General Overseer of Testimony Chapel na garin Ilori ya kuma ja hankalin gwamnatocin kasar a kowane mataki da su tabbatar da sun samar wa matasa ayyukan yin wanda rashin sa ne ke jefa su cikin sana'ar ta karuwancin.

KU KARANTA: An fitar da wata 'yar majalisa waje saboda shigar banza
Legit.ng ta samu dai cewa shehin malamin ta Kiristanci yayi wannan jawabin ne a garin Ilori inda kuma ya bayyana cewa duk macen da ta maida karuwanci a matsayin sana'a to kam tabbas tabewar duniya ta gama sauka a kanta.
A baya ma dai mun kawo maku wani labarin yadda jama'a mazauna garin Abuja babban birnin tarayya ke kokawa game da yawaita karuwai da kuma 'yan daudu a garin yayin da kuma suka bukaci Gwamnati da ta shigo cikin lamarin domin yiwa abun tufka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng