Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata
Wani matashi mai suna Seun ya gamu da ajalinsa a hannun budurwarsa mai suna Adesuna Osazuwa, bayan ta caka masa almakashi a kirji a jihar Legas.
Jaridar Daily Post ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a rukunin gidaje na Gowon, dake Egbeda, jihar Legas, inda masoyan suka samu takaddama bayan ta kama shi yana hira da wata yarinya a manhajar Whatsapp.
KU KARANTA: Gwamnati bata da nufin yi ma Atiku bita-da-ƙulli, gyara muke yi – Inji Hadiza Bala Usman
Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito ana zargin yarinyar da kwankwadar kayan maye kafin ta aikinta ma saurayinta wannan ta’asa.
Wani ma’abocin facebook yace “Masoyan sun fara fada ne akan zargin cin amana da budurwar ke yi ma saurayin, inda nan da nan ta dauko almakashi ta caka masa a kirji, nan take ya fadi matacce.”
Bincike ya nuna Seuna ya gamu da mutuwarsa a hannun Adesuwa ne, kwanaki biyar bayan ya taya ta murnan zagayowar ranar haihuwarta, inda ya sake jaddada soyayyarsa gar eta a shafin Facebook.
A yanzu dai Yansanda sun cika hannu da Adesuwa, yayin daka garzaya da gawar Seun dakin ajiyan gawa. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Yadda shari'ar Nnamdi Kanu ta kasance, kalla a Legit.ng TV
Asali: Legit.ng