Jagwal: Wani mutumi ya ɗauki alhakin yi ma Uwa da Ýarta ciki a lokaci ɗaya

Jagwal: Wani mutumi ya ɗauki alhakin yi ma Uwa da Ýarta ciki a lokaci ɗaya

Rundunar Yansandan jihar Legas, sun yi caraf da wani mutumi mai shekaru 36, Saka Akonda bayan da ya dirka ma yar cikinsa ciki, mai shekaru 13.

Legit.ng ta ruwaito ita kanta matar Mutumin na dauke da ciki watanni 6, sa’annan ya mutumin ya lallaba yayi ma yarta ciki, dayake ba shi bane mahaifinta, agola ce.

KU KARANTA: Dala biliyan 30: Buhari ya baiwa gwmanan jihar Jigawa, gagarumar aiki

Kawun yarinyar ne ya kai karar Saka ga hukumar Yansanda, inda ba tare da bata lokaci ba suka kamo shi, kuma suka gurfanar da shi gaban kotu bayan da suka kammala gudanar da bincike.

Jagwal: Wani mutumi ya ɗauki alhakin yi ma Uwa da Ýarta ciki a lokaci ɗaya
Jagwal

Sai dai Mutumin yace shi fa yana matukar kaunar yarinyar, kuma ya cika da mamakin yadda Yansanda suka kama shi, duk da cewa ya sansanta matsalar da mahaifin yarinyar na asali, kuma ya kara da cewa ya amince zai dauki nauyin duk abinda yarinyar ta haifa.

“Da farko mun sasanta da mahaifin yarinyar, amma kaninsa ne ke kunan wutan rikicin, don haka nek rokon mahaifin yarinyar daya min hakuri, kuma kada ya manta ni nake daukan dawainiyar yarinyar sama da shekara 5 da suka wuce.” Inji shi.

Shi kuwa kawun yarinyar ya shaida ma kotu cewa “Matar yayana ne ta auri wannan mutumin banzan, wanda yayi da da ya ciki a lokaci daya. don haka nake bukatar ganin kotu tayi masa hukuncin daya dace da shi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

We need to understand the Biafra objective, Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: