Manyan dalilai guda 6 da ka iya sanya mace haifan jarirai ‘Bakwaini’
Wani shahararren masanin aikin likitanci mai kula da kiwon lafiyan mata Dakta Chris Abumchi ya bayyana Najeriya a matsayin kasar ta uku cikin kasashen da aka fi haihuwar Bakwaini.
Jaridar Premium Times ta ruwaito likitan yana fadin cewa a duk haihuwa 10, ana samun jariri bakwaini guda 1.
KU KARANTA: Ashsha! Uwargida ta kashe mijinta saboda neman matan aure
Majiyar Legit.ng ta ruwaito likitana ya yi bayanin haihuwa bakwaini a matsayin yadda ake haihuwar jariri ba tare da wasu sashin jikinsa sun kammala haduwa ba, sakamakon haihuwarsa kafin watanni 9.
Dakta Chris yace dalilan dake sa ake haihuwa Bakwaini sun hada da:
1. Shan taba sigari
2. Mace mai ciwon siga
3- Amfani da magunguna ba tare da izinin likita ba
4- Mace mai shan giya
5- Zama da yunwa
6- Rashin samun kwanciyar hankali
Da wannan ake yin kira ga mata da masu dauke da juna biyu da su dinga zuwa Asibiti da zarar sun fara zubar da jini ko jin ciwon jiki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng