Biyafara: IPOB kungiyar yan ta’adda ne; Fulani makiyaya kungiyar masu laifi ne kawai – Fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa tace akwai banbanci tsakanin ayyukan makiyaya da ta IPOB
- Garba Shehu yace kungiyar masu fafatukar kafa Biyafara (IPOB), kungiyar yan ta’adda ne sannan Fulani makiyaya kuma kungiyar masu laifi ne
- A cewar sa kungiyar masu fafatukar Biyafaran bata nuna ladabi ba ga kundin tsarin mulkin Najeriya
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a ranar Alhamis yace kungiyar masu fafatukar kafa Biyafara (IPOB), kungiyar yan ta’adda ne sannan Fulani makiyaya kuma kungiyar masu laifi ne.
Kakakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan talabijan din Channels yayinda yake magana kan nadi da aka yi wa kungiyar IPOB dake karkashin shugabancin Nnamdi Kanu kwanan nan.
Shehu ya lura cewa kungiyar masu fafatukar Biyafaran bata nuna ladabi ba ga kundin tsarin mulkin Najeriya.
Yayinda yake mayar da martani kan me yasa ba’a nada Fulani makiyaya ba duk da cewan suna kashe-kashen yan Najeriya, Garba ya amsa da cewa, “akwai banbanci tsakanin kungiyar masu laifuka da ayyukan ta’addanci.
KU KARANTA KUMA: Zaben 2019 ba zai yiwu ba – Inji Apostle Suleman cikin sabon wahayi
“Fulani makiyaya kungiya ce na masu laifi kuma muna magance al’amarinsu bisa dokar kasa amman kungiyar IPOB kamar kungiyar Boko Haram suna da yankuna da suka kafa wa kansu a matsayin yankuna masu zaman kansu sun kuma suna shirye don kai wa makofcin jihohi farmaki.
“Sun daga damuwarsu a jihar Kogi, Benue sun kuma bayyana ra’ayinsu kan jihar Bayelsa da Rivers. Wannan ya kasance daidai da abunda kungiyar Boko Haram suka yi da tutarsu da kuma tsarin haraji. Lallai wadannan abubuwan sun saba wa dokar kasa.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng