Lafiya uwar jiki: Amfanin abarba 13 a jikin dan adam

Lafiya uwar jiki: Amfanin abarba 13 a jikin dan adam

Musamman ma kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya.

Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.

Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam saboda tana dauke da muhimman abubuwa; fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.

Wadannan sinadarai dai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.

Legit.ng da ta zakulo maku kadan daga amfanin Abarba:

1. Tana dauke da sinadarin

magnees da calcium wanda ke kara karfin kashi

2. Tana dauke da anti oxidant wanda ke kara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.

3. Tana maganin mura da sanyin kirji.

Lafiya uwar jiki: Amfanin abarba 13 a jikin dan adam
Lafiya uwar jiki: Amfanin abarba 13 a jikin dan adam

KU KARANTA: An fanin rake 9 a jikin dan adam

5. Tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka.

6. Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.

7. Tana kara lafiyar dasashi da kare hakora.

8. Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.

10. Tana maganin tsutsar ciki.

11. Tana kara ma idanu lafiya

12. Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya

13. Tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa

da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel