Ra’ayi: Musulinci a tsakanin Mubarak Bala Da Abubakar Shekau (I) daga Aliyu Dahiru Aliyu

Ra’ayi: Musulinci a tsakanin Mubarak Bala Da Abubakar Shekau (I) daga Aliyu Dahiru Aliyu

Tambihin Edita: Yayinda Abubakar Shekau ya saki sabuwar bidiyo game da gazawar hukumar soji wajen kamashi, wani marubucin yanar gizo ya mayar da martani ga Shekau amma wasu mabiya addinin Islama sun ga hakan a matsayin suka ga addinin Musulunci ba ga Shekau din kan sa ba. Saboda haka wani marubucin, Aliyu Dahiru ya bayyana abinda ya fahimta da rubutun.

Wannan rubutun ra’ayin marubucin ne ba ra’ayin Legit.ng

Ra’ayi: Musulinci a tsakanin Mubarak Bala Da Abubakar Shekau (I) daga Aliyu Dahiru Aliyu
Ra’ayi: Musulinci a tsakanin Mubarak Bala Da Abubakar Shekau (I) daga Aliyu Dahiru Aliyu

Matsalar mulhidai irinsu Mubarak Bala shine sun fahimci addini irin yadda su Abubakar Shekau suka fahimta. Addini a matsayin kisa, zubar da jini, tashin hankali, ci-baya, yakar ilimi da rashin yanci. Yayinda su Abubakar Shekau ko Abubakar Albaghdadiy suke yanka mutane, su kuma suna ganin addinin shine yanka mutanen! Wannan rashin adalcine da kuma yiwa mabiya addinai kudin goro wajen cewa suna aikata ta'addanci a matsayin addini. Idan ko hakane zamu iya cewa abinda mulhidai sukai irinsu Benito Mussolini na kisan kare dangi da kashe mutane a yakokinsu to shine ilhadi! Zamu iya cewa abinda mukafi tsoro a wannan zamanin, wato makamin kare dangi na nukiliya wanda Albert Einstein shine yayi sababin kawoshi a kimiyyance, shima kimiyyane! Kuskurene muce abinda Lord Resistance Army ko Adolf Hitler sukai a Uganda koyarwar kiristancine. Kuskurene muce zalincin da Zionist suke a Israel akan raunanan Palestine shima koyarwar addinin yahudancine. Kuskurene muce abinda wasu tsirarun yan addinin Buddhism suke aikatawa musulman Rohingya yana nufin shine addinin.

Dukkanin wadannan addinai da na lissafa a sama suna koyar da zaman lafiya da soyayya. Sai dai a ko'ina ba'a rasa azzalumai da suke fakewa da sunan wani addini ko kungiya ko ilimi wajen zalintar raunana. Addinin Buddha na Gotama Buddha a misali an sanshi da zaman lafiya da rashin neman rigima kuma akan haka ya dora falsafarsa kuma mafi yawan mabiyansa a haka aka sansu. Litattafan addinin kamar irinsu "Sutta-Pitaka" da "Tripitaka" da za'a iya samun bayanan Gotama Buddha aciki, wanda an tattaresu acikin wasu mujalladan litattafai da ake kira "Sacred Books of the Buddhists", sun nuna addinin na zaman lafiyane da hakuri. Don haka ake mamakin ya akai Adolf Hitler ya dauki tambarin addinin (swastiika) da yake nuna zaman lafiya kuma yayi amfani dashi wajen kisan kiyashin da ya yayiwa yahudawa. Saboda haka, samuwar irinsu Ashin Wirathu ko Aun San Suu Kyi da suke taimakon kisan kiyashin da akewa musulmi acikin addinin baya nufin cewa falsafar addini ta koma ta tashin hankali. Zamu zargi mutumne da kwadayinsa na zubar da jini amma ba addininsa da dama ya hanashi aikata hakan ba. Duk son zaman lafiyar Mohatma Mohandis Gandhi karshe dan addinin Sikh ne ya kasheshi. Shin addinin Sikh zamu zarga ko mutumin da yayi kisan? Bayan an harba nukiliya a kasar Japan kan Hiroshima da Nagasaki, shin kimiyya da Albert Einstein zamu zarga ko kuma America da ta harba makamin? Idan su Abubakar Shekau sunyi amfani da fasahar sadarwa (YouTube a misali) wajen tsorata mutane, shin fasahar zamu zarga ko kungiyar Boko haram?

Haka shima addinin kiristanci, kowa yasan addinin da takensa na soyayya. Yesu Almasihu dakansa ya koyar da cewa koda an mareka to ka juya fuskarka a karamaka don kada ka batawa mai dukanka rai! Amma a haka ba'a rasa yan ta'adda acikin addinin kamar su Adolf Hitler a Germany ko kungiyar Lord Resistance Army a Uganda ba. Shin hakan na nufin koyarwar kiristanci ne? Kiristanci daban da abinda yan ta'adda suka fake da addinin suka aikata. Dan adam yana da son rai tun asali. Duk lokacin da yaga yana da karfi to sai yayi kokarin cin zalin na kasa dashi. Hatta a duniyar ilhadin a haka mutane suke. Lokacin da Karl Marx ya fito yana yakar masu kudi da azzaluman addini, shi ake zalinta da raunana. Amma bayan ya samu karfi da taimakon Lenin da zuwa irinsu Joseph Stalin a Russia sai suka koma zalintar raunana a Afghanistan da sunan kwamunisanci. Da taimakon America, kungiyar Taliban da Osama bn Laden tayi karfi suka raunana taraiyar Soviet sai suka koma zalintar wasu da sunan addini. A haka dan adam yake aikata abinda yaga dama amma sai ya fake da addinai ko fahimtoci.

Ina yimaka uzurin cewa baka fahimci addinin musulincin da aka haifeka acikinsa ba balle falsafar sauran addinan. Ka tashi a inda ake hana tambayoyi da sunan addini kuma ake zalinci da sunan shari'a. Shari'ar da ka fahimta, irinta Shekau, ba itace shari'ar musulinci ba. Shari'ar da akai a Zamfara wacce ta kyale masu satar miliyoyi daga yan siyasa kuma ta yankewa barawon saniya hannu, ba itace shar'iar da musulinci yace ayi ba. Ubangijin da kake zato mai kama da mutane (anthropomorphic) ba shine Ubangijin musulinci ba. Fahimtar da kayiwa Allah (anthropocentric) ba itace fahimtar tauhidin musulinci ba. Yakokin da kake cewa sahabbai sunyi, ina so ka gane cewa a tsarin dokar musulinci aikin sahabi ba hujja bane. Ni akan kaina nafi ganin abinda sukai a matsayin mulkin mallaka (colonialism) amma ba tsarin musulinci da yace babu dole a addini ba. Kafin ka shiga halin da ka shiga na musa Allah da yakar addinai ni kaina na taba samun irin wannan shakkun (waye bai taba samu ba?!). Banbancina dakai shine ni banyi gaggawar cewa shikenan babu Allah ba. Abinda kayi shirmene a falsafa da ake kira "Category Mistake" wato rashin samun abu bayan ka bincika sai kace babu shi baki daya! Kuma irin wannan abin da kake shine ake kira "argumentum ad ignoratiam", saboda ka rasa wanda zaimaka bayanin abu sai kace karyane! Anan ba bayani zanmaka don ka koma musulinci ba, bayani zanmaka don ka gane baka fahimci addinin musulincin da kake yaka kuma kake kwatantashi da ayyukan yan ta'adda kamar Shekau ba.

Da farko zan fara nunamaka cewar addinin musulinci ya bawa kowa yancin yayi addininsa kuma babu dole acikinsa ((Q2:256)). Hatta Manzon Allah (saw) ya fada a ayoyin Alqur'ani ba babu adadi cewa da Allah yana so da ya maida kowa musulmi, don haka baya tilasawa kowa sai yazama mai imani dashi ((Q10:99)). Sannan Alqur'ani ya fadamana cewa kowa yana da yancin ya zabi inda yaga damar yi amma zai tarar da hukunci a ranar lahira ((Q10:108)). Sannan a Alqur'ani ((Q4:137)) Allah ya bamu labarin wadanda sukai imani sannan suka kafirce, sannan suka kara imani kuma suka kara kafircewa, suka kara imani sannan suka kara kafirce! Amma ba abinda Annabi (saw) yayimusu na kisa. Duk bakaga wadannan ba sai hadisi guda daya da baka iya rubutashi daidai ba?! Duk bakaga yadda Allah yabada yancin addini a ayoyi sama da 100 ba sai hadisi guda daya da dama ana tantamar ingancinsa? Wadanda suka aminta da ingancinsama sunyi tawilinsa maimakon daukar lafazinsa (literally).

Hadisin yazo acikin "Sahihul Bukhari" da karamin littafin "Arabeen An-nawawy" da sauransu cewa Manzon Allah (saw) yace "An umarceni da na yaki 'mutane' har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah". Tare da cewa hatta Ibn Hajar a littafinsa na "Fathul Bariy" a sharhin da ya yiwa "Sahihul Bukhari" ya tabbatar da cewa akwai matsala ta fuskar sanadin hadisin (sanadin hadisi shine yake nuna ingancinsa ko rashin ingancinsa ta wata fuskar). Amma koda ya inganta to me ake nufi da kalmar 'mutane' a hadisin? Bisa ilimin falsafar yare (linguistic philosophy) da kuma "Logical positivism" kalmar 'mutane' itace zata gayamana me hadisin yake nufi domin ayyukan Annabi (saw) ya nuna cewa dole muna bukatar sanin me kalmar ke nufi tunda Manzon Allah dai ya zauna da wadanda basu yarda Allahn shine abin bautarsu ba kuma bai yake su ba. Acikin Madina akwai yahudawan Banu Qurayza da Banu Nadhir wadanda ba musulmi bane kuma Annabi bai kashesu duka ba. Hasalima a musulinci akwai tsarin "jizya" da wanda bai yarda da Allah ba zai dinga bayarwa don yayi addininsa kuma a bashi tsaro da kulawa a kasar musulinci. Da ace gayar ko matukar abinda ake bukata shine ayi imani da Allah ko a kashe mutane dukansu to da babu yadda za'ai ayi sulhu da kiristocin Najran kuma babu yadda za'ai Umar bn Khattab ya kyale coci a Palestine! Abinda kalmar 'mutane' take nufi anan sune wadanda suka fara yakar musulmi ba wai dukan mutane ba. Tun asali a addinin musulinci babu yaki sai ga wadanda suka fara yakar musulmi ((Q22:39)) ko kuma wadanda suka kori musulmi daga garuruwansu suka hanasu yancin addini ((Q22:40)) don haka zasu yaki wadannan mutane har sai ya zamana babu zalincin akan kasa kuma addini ya zama na (tsarin) Allah ((Q2:190)). Tsarin Allah shine a bawa kowa yancin addininsa kuma ayi adalci a daina zalinci a ban kasa.

Akwai cigaba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel