Karanta Ka Qaru: Ko kun san Jihar da ta fi kowace yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya a Najeriya?
- Gwamnatin tarayya ce gaba a bangaren samar da ayyuka a kasa
- Yankin kudu maso gabas ne ya fi kowanne yanki yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya
- Yankin arewa maso yamma ne ke da karancin yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ce gaba a bangaren samar da ayyuka a kasa. Duk lokacin da gwamnatin tarayya za ta dauki aiki ta kan yi raba dai-dai ne tsakanin jihoshin Najeriya. A wata kididdiga da tsohon shugaban sashen kula da bunkasa ayyukan gwamnatin tarayya, Dakta Joe Abah, ya fitar ta nuna adadin jimillar ma'aikatan gwamnatin tarayya da ke karkashin ma'aikatun tarayya da kuma kason da kowacce ke da shi.
Ga adadin ma'aikatan da kowace jiha ke da su da kuma jimillar ma'aikatan kamar yadda Joe Abah ya wallafa;
Jihar Imo 5,825
Jihar Kogi 5,186
Jihar Ogun 4,669
Jihar Delta 4,419
Jihar Akwa Ibom 4,416
Jihar Benue 3,951
Jihar Edo 3,890
Jihar Abia 3,579
Jihar Anambra 3,576
Jihar Kaduna 3,199
Jihar Ondo 3,393
Jihar Oyo 3,244
Jihar Osun 3,321
Jihar Enugu 2,695
Jihar Cross River 2,681
Jihar Ekiti 2,613
Jihar Plateau 2,542
Jihar Kwara 2,537
Jihar Niger 2,193
Jihar Lagos 2,180
Jihar Borno 1,822
Jihar Adamawa 1,727
Jihar Rivers 1,675.
DUBA WANNAN: Babbar Sallah a Jihar Borno: Labari cikin Hotuna
Jihar Kano 1,545
Jihar Nasarawa 1,452
Jihar Katsina 1,237
Jihar Gombe State 1,218
Jihar Bauchi 1,172
Jihar Taraba 1,112
Jihar Bayelsa 957
Jihar Kebbi 875
Jihar Ebonyi 865
Jihar Yobe 744
Jihar Sokoto 732
Jihar Jigawa 675
Jihar Zamfara 543
Sannan sai wasu mutum 518 da ba a tantance jihoshin da suka fito ba. Jimillar ma'aikatan ya kama 89,511.
Yankin kudu maso gabas na da kaso 18.47% na yawan ma'aikatan, sai yankin kudu maso kudu da kaso 20.15%, san nan kudu maso yamma na da kaso 21. 69%, a yayin da arewa ta tsakiya ta samu kaso 19.95%, arewa maso gabas tana da kaso 10.44%, sai arewa maso yamma da kaso 9.83%.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng