Abin ban dariya:Obasanjo ya koma alkalancin Ƙwallo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tuna baya inda ya zanzare ya shiga fili don a fafata da shi.

Hakan ya faru ne kuwa a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba sa’ailin da shi Obasanjo yayi alkalanci wasa wato lafari a wani wasan sada zumunta tsakanin likitoci a filin wasa na tunawa da Moshood Abiola dake garin Abekuta na jihar Ogun.
Sai dai kamar yadda aka san Obasanjo, mutum ne bai barkwanci, a nan ma bai yi kasa a gwiwa ba, sai daya dana barkwancin yayin da yake gudanar da aikinsa na alkalin wasa, wasan da aka buga tsakanin likitoci mata da likitoci maza.

KU KARANTA: Osinbajo da Uwargidarsa sun yi bikin cikar shekaru 27 da aure
Obasanjo ya nuna kwarewarsa da sanin dokokin kwallo yayin alkalancin, hakan ya sanya yan kallo shan dariya yayin da wasan ke gudana musamman lokacin da alkalin wasa Obasanjo ya nuna ma wani dan wasa shudin kati na gargadi, da lokacin da aka tadiye wani dan wasa a cikin gida wanda hakan ya sanya shi hura bugun daga kai sai gola.
Sai dai daga karshe, bayan an fafata, an gwabza tare da yin gumurzu, likitoci mata sun lashe wasan ci 2 da 1.
Ga wadanda basu sani ba Olusegun Mathew Okikiola Aremu Obasanjo ya taba zama tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, sa’annan ya sake zama shugaban kasar farar hula daga 1999 zuwa 2007.
Zaku iya samun mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng