Abubuwa 5 game da marigayi Ibrahim Dasuki
- Allah ya yi wa Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a daular Usmaniyya da ke Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki rasuwa
- Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu ne ranar Litinin da daddare a wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93
- Wata majiya a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta shaida wa majiyar mu cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana'izarsa kuma ana sa ran gudanar da ita da misalin karfe 2:00 na ranar Talata a birnin na Sakkwato
Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa.
Kafar labaran ku ta Legit.ng ta zakulo maku wasu muhimman al'amurra guda 10 da ya kamata ku sani game da shi mari gayin.
(1) Mai alfarma Alhaji Ibrahim Dasuki shi ne Sarkin Musulmi na 18 a jerin sarakunan Daular Usmaniyya.
Kafin zamowarsa sarkin musulmi a shekara ta 1988, ya rike sarautar Baraden Sakkwato matsayin da ya yi amfani da shi wajen bayar da gudunmuwa wurin kafa kungiyar Jama'atul Nasril Islam.
(2) Shi ne dai Sarkin Musulmi na farko daga Zuri'ar Buhari dan Sheikh Usman Bin Fodiyo, kuma kawo yanzu shi kadai ya yi sarautar ta Sarkin Musulmi daga wannan gidan.
An haife shi ne a garin Dogon Daji na jihar Sakkwato a shekarar 1923.
Da ne ga Haliru dan Barau wanda ya rike sarautar Ubankasar Dogon Daji wato Sarkin Yamma Dogondaji.
Ya yi karatun addinin Musulunci da na elementare a garin na Dogondaji kafin daga bisa ni ya tafi kwallejin Middle School ta Sakkwato da kuma ta Barewa da ke Zariya inda ya kammala karatunsa na Sakandare a 1943.
(3) Tsakanin shekarun 1965 zuwa 1988 da aka nada shi sarauta, Alhaji Ibrahim Dasuki ya fi mayar da karfi ne ga harkokin kasuwanci.
Marigayin ya zama Sarkin Musulmi ne a watan Disambar shekara ta 1988 bayan rasuwar Sarkin Musulmi na 17 Alhaji Abubakar Sadik na III
Sanar da shi a zaman magajin Sarki Abubakar na III a maimakon dansa Alhaji Muhammadu Maccido Abubakar III ya jawo wata zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyar a birnin na Sakkwato wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma.
Masu adawa da nadinsa a lokacin na ganin Muhammad Maccido mai ra'ayin mazan jiya a zaman wanda ya fi cancantar da wannan kujerar bisa shi Alhaji Ibrahim Dasuki mai ra'ayin tafiya da zamani.
(4) Ya kwashe shekaru takwas kan mulki kafin gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha ta sauke shi a shekara ta 1996.
An zarge shi da kin bin umarnin gwamnati da kuma yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba tare da neman izni ba.
Bayan sako shi daga wurin da aka tsare shi a jihar Taraba na tsawon shekaru, ya tare a gidansa da ke birnin Kaduna inda ya ci gaba da tafiyar da harkokin rayuwarsa har zuwa lokacin ya kamu da cutar ajali.
(5) Marigayin ya nuna rashin jin dadinsa karara, lokacin da jami'an tsaro suka kai sumame gidansa na Sokkwato a lokacin da suke binciken dansa Sambo Dasuki.
Shi dai Sambo, wanda tsohon mai baiwa Shugaba Goodluck Jonathan shawara ne kan harkokin tsaro, yana fuskantar shari'a kan zargin cin hanci da rashawa.
Batun da ya musanta yana mai cewa siyasa ce kawai.
Allah ya yi wa Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a daular Usmaniyya da ke Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki rasuwa.
Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu ne ranar Litinin da daddare a wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93.
Wata majiya a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta shaida wa BBC cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana'izarsa kuma ana sa ran gudanar da ita da misalin karfe 2:00 na ranar Talata a birnin na Sakkwato.
Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng