SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

- Rashin sani yasa mutane basa shan ruwa da sassafe

- Shan ruwa kafin cin komai hanya ce mai sauki domin samun karuwar lafiya

Fara shan ruwa kafin cin komai da sassafe na taimakawa wajen kare mu daga cututtuka da dama daga ciki akwai:

Ciwon kai, ciwon jiki, saisaita bugun zuciya, raguwar kiba, zazzabin hunhu, ciwon numfashi (Asthma), tarin Shika, kyanda , ciwon Koda da na bututun mafitsara, Amai (Haraswa) da gudawa, ciwon sukari da cushewar ciki da duk nau’ikan matsalar ido da na mafitsara, da rikecewar al’adar mata da ma matsalar kunne da hanci da kuma makogwaro.

Ga yadda ake amfani da shi:

Da zarar ka farka da safe, kafin ka wanke bakinka da aswaki ko burushi, sai ka sha ruwa kwatankwacin kofin gilashi hudu (4) kwantankwacin 640 ml, daga nan sai a wanke bakin amma kar da a zauna sannan kar da a ci ko shan komai har sai bayan tsawon mintuna arba’in da biyar, daga nan kuma ana iya ci ko shan duk abin da ake so.

Bayan ka ci abincin rana da na dare, to kar da ka ci komai har na tsawon awanni biyu da daddare.

Amma ga tsofaffi ko marasa lafiya da ba za su iya shan kofin gilashi hudu na ruwan ba, to suna iya farawa da ko kadan ne, gwargwadon yadda zasu iya, daga bisani sai su na karawa har ya kai adadin da aka fada a sama. Mutukar aka bi wannan shawara, zata taimaka matuka wajen bayar da kariya daga cutuka masu yawan gaske sannan kuma da karin amfanuwa da abubuwan da ruwa ke bawa gangar jiki.

Shin har tsawon wane lokaci ake yin hakan?

Ga masu hawan jini, sai suyi wannan tsari har na tsawon kwanaki talatin (30)

Masu matsalar rashin iya cin wadataccen abinci, za su yi na tsawon kwanaki goma (10) ne kacal

Ciwon sukari kuwa, ana yin irin wannan shan ruwa ne shi ma har na tsawon kwanaki talatin (30)

Cushewar ciki da rashin narkewar abinci, ana yi ne tsawon kwanaki goma (10) kacal

Ga masu tarin TB (Shika), sai su yi irin wannan shan ruwa shi ma har na tsawon kwanaki talatin (30).

Sai dai idan son samu ne, kamata yayi idan aka fara wannan shan ruwa a cigaba har tsawon rayuwa batare da dakatawa, domin cigaba da samun cikakkiyar lafiya da kwarin jiki.

Abubuwan amfani da shan ruwa kafin komai ke kawo wa

Kashe sinadarin gubar jiki.

Da zarar mun sha ruwa, jikinmu kan warwasa musamman ta hanyar bawa kayan cikinmu damar gudana cikin sauki, kuma sai ya koro duk wadansu sinadarai masu cutarwa hanyar fita waje, shan ruwa kafin cin komai kan karasa aikin korar sinadaran na guba zuwa wajen jiki. Shan wadataccen ruwa na samar da karuwar sinadaran gina jiki da kuma samar da kwayoyin halittar jinni.

Taimakawa jiki wurin narkar da abinci

Saukakawa jikin wajen wahalar da yake sha yayin narkar da abinci da kimanin kashi 24%, hakan kuma zai yi mutukar taimakawa maras lafiya musamman wadanda likita ya tsarawa abinda zasu na ci.

KU KARANTA:Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki

Rage kiba

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Sakamakon wanke jiki da shan ruwa kafin cin komai yake yi daga sinadaran gubar jiki, wanda hakan ke taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abincin, hakan zai sanya rashin jin yunwa da kuma sha’awar cin abincin da sauri wanda hakan kan kare mu daga yin kiba da nauyi musamman ga masu dabi’ar ci sosai.akamakon wanke jiki da shan ruwa kafin cin komai yake yi daga sinadaran gubar jiki, wanda hakan ke taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abincin, hakan zai sanya rashin jin yunwa da kuma sha’awar cin abincin da sauri wanda hakan kan kare mu daga yin kiba da nauyi musamman ga masu dabi’ar ci sosai.

Konewar zuciya

Sakamakon wanke jiki da shan ruwa kafin cin komai yake yi daga sinadaran gubar jiki, wanda hakan ke taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abincin, hakan zai sanya rashin jin yunwa da kuma sha’awar cin abincin da sauri wanda hakan kan kare mu daga yin kiba da nauyi musamman ga masu dabi’ar ci sosai.akamakon wanke jikiburnhan ruwa kafin cin komai yake yi daga sinadaran gubar jiki, wanda hakan ke taimakawa sassan jikinmu wajen narkar da abincin, hakan zai sanya rashin jin yunwa da kuma sha’awar cin abincin da sauri wanda hakan kan kare mu daga yin kiba da nauyi musamman ga masu dabi’ar ci sosai.

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Mukan ji zuciyarmu kamar ta kama da gobara wasu lokutan, hakan na fauwa ne a dalilin karancin sinadarin yawun dake taimakawa wurin narkar da abinci, shan ruwa kafin cin komai na taimakawa wajen samuwar wannan sinadarin da zai magance matsalar da kuma kimtsa jiki kafin cin kumallo.

Gyran fata da shekin jiki

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Karancin ruwa a jiki na haifar da tauyewa da kuma tsofar da mutum cikin sauri, kamar yadda bincike ya nuna, shan ruwa cikin babban kofi kamar kimanin (500 ml) kan taimaka sosai wurin gudanar jini cikin sauki da kuma gyaran fata, ta rika sheki da kyalli tare da santsi.

Karin gashi da sanya shi santsi

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Rashin ruwa a jiki ba karamar illa gare shi ga jiki ba, samuwarsa kuwa na taimaka wurin girma da kyawun jiki ko akasin hakan. Karancin shan ruwa kan haddasa motsewar sassa daban-daban na jiki ciki har da gashi daga ciki da ma wajensa, musamman ga mata. Saboda haka shan ruwa na da alfanu matuka musamman idan aka sha kafin cin komai da safe.

Matsalar koda da mafitsara

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Shan ruwa da zarar an farka yana da muhimmanci matuka wajen bayar da kariya daga kamuwa daga cutar koda da kuma na mafitsara. Shan ruwan sassafe na korar da duk wasu sinadarai marasa amfani masu guba da ka iya bawa koda da mafitsara matsala. A takaice gwargwadon shan ruwanka gwargwadon morewa wannan sinadarin da ke wankin gubar jikin.

Karfafa garkuwar jiki

SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE
SIRRUKA TAKWAS NA SHAN RUWA DA SASSAFE

Shan ruwa kafin cin komai na karfafa garkuwar jiki wurin samun karfin yakar rashin daidaiton yadda jiki yake aiki wanda hakan ke taimakawa wurin yakar cutuka daban-daban da kuma bayar da kariya daga saurin kamuwa daga rashin lafiya.

Mai karatu, ka dai ji irin alfanun dake cikin shan ruwa da zarar an farka kafin cin komai, a saboda haka babu tantama hanya ce mafi saukin bi domin kawo sauyi cikin lokaci kalilan ga yadda jiki yake aiki, ba tare da kashe kudi mai yawa ba, sai dai kawai in za’a sha ruwan a tabbata an sha mai tsafta sosai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng