Yan kwallo 5 da suka fi zura kwallaye a nahiyar Turai (Hotuna)
Gasar wasannin tamaula ta bana ta fara yin nisa a wasu kasashen nahiyar Turai, wanda tuni wasu 'yan wasan suka yi gaba wajen zura kwallaye a raga.
1. Bari mu fara da gasar Premier wadda aka yi wasannin mako na 22, inda Chelsea ke kan gaba a teburi da maki 55.
A gasar ta Premier Diego Costa na Chelsea da Alexis Sanchez na Arsenal sune ke kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar, inda kowannensu ya ci 15.
2. Gasar La Liga ta Spaniya an buga wasannin mako na 19, inda Real Madrid ce ta daya a kan teburi da maki 43.
'Yan wasan Barcelona Lionel Messi da Luis Suarez kowannensu ya ci kwallaye 15, sune ke mataki na daya a yawan zura kwallaye a gasar.
3. A Serie A ta kasar Italiya an yi wasanni 21, inda Juventus ke mataki na daya da maki 48, kuma tana da kwantan wasa daya.
Dan kwallon Inter Milan Mauro Icardi shi ne ya ci kwallaye 15, sai Andrea Belotti na Torino a matsayi na biyu wanda ya ci kwallaye 14 a raga.
4. A gasar Bundesliga ta Jamus Bayern Munich ce ta daya da maki 42, bayan da aka yi wasannin mako na 17.
Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund ya ci kwallaye 16 sai Robert Lewandowski na Bayern Munich da ya ci 14 a raga.
5. A Faransa kuwa a gasar Ligue 1 an yi wasannin mako na 21, kuma Monaco ce ta daya a kan teburi da maki 48.
Edison Cavani na Paris St Germain ne a matsayi na daya da kwallaye 20, sai Alexandre Lacazette na Lyon da ya ci 17.
Asali: Legit.ng