UEFA ta fito da jerin wasannin da za a buga a zagaye na gaba a Turai

UEFA ta fito da jerin wasannin da za a buga a zagaye na gaba a Turai

Dazu nan aka fito da jadawalin zagaye na gaba na karawar da za ayi a Gasar cin kofin Nahiyar Turai. Kungiyoyin da su ka samu kai wa ga nasara sun san abokan karawarsu a halin yanzu.

1. Real Madrid v Manchester City

Manchester City za ta kara da kungiyar Real Madrid a wannan zagaye na kungiyoyi 16 da su ka rage. Pep Guardiola ya fito ne a matsayin na farko a rukuninsa. Wannan wasa zai yi budu sosai.

2. Chelsea v Bayern Munich

Wani wasa da jama’a za su kosa a buga shi ne na Chelsea da Bayern. Chelsea sun iya fitowa ne daga rukunin farko da kyar a makon jiya. Bayern kuma sun yi nasara a duka wasanninsu.

3. Dortmund v PSG

Kungiyar Dortmund da ta fito tare da Barcelona za ta fafata da Zakarun kasar Faransa watau PSG a sabuwar shekara. PSG kuma ta sha gaban Real Madrid a teburin rukunin farko a kakar bana.

KU KARANTA: Ronaldo ya rage zafi da kyautar gida bayan Messi ya ci Ballon D'or

4. Liverpool v Atletico Madrid

Zakarun bana, Liverpool za su fara kare kambunsu ne a wajen Atletico Madrid wanda su ka biyo Juventus a baya a rukuninsu. Wannan wasa ya na cikin masu ban kayen da ake sa ran kallo.

Ga cikakken hadin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta UEFA ta yi a yau 16 ga Watan Disamban 2019.

Borussia Dortmund da Paris Saint-Germain

Real Madrid da Manchester City

Atalanta da Valencia

Atletico Madrid da Liverpool

Chelsea da Bayern Munich

Lyons da Juventus

Tottenham da RB Leipzig

Napoli da Barcelona

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel