UEFA ta fitar da ‘Yan kwallon shekarar bana, ba a maganar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo

UEFA ta fitar da ‘Yan kwallon shekarar bana, ba a maganar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo

  • Hukumar UEFA ta fito da jerin taurarin ‘yan wasan kwallon kafa na shekarar nan
  • A wannan karo babu sunan Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a jerin ‘yan kwallon
  • Thomas Tuchel da Pep Guardiola za su gwabza a wajen samun kyautar kocin bana

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta fitar da jerin ‘yan wasan da ake sa rai daga cikin su za a samu gwarzon ‘dan wasan shekarar 2020/21.

A wannan karo, babu sunan ko daya daga cikin taurarin da aka saba gani, ‘dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo da ‘dan wasa Lionel Messi.

UEFA ta ce za ta sanar da wadanda suka yi nasarar lashe kyaututtukan bana a ranar 26 ga watan Agusta, 2021, a garin Istanbul, kasar Turkiyya.

‘Yan wasan shekara (Maza)

A rukunin gwarazan ‘yan kwallon kafa na bana, an fitar da jerin ‘yan wasa uku wadanda daga cikinsu za a fito da wanda zai samu kyautar 2020/21.

Wadannan ‘yan wasa su ne:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kevin DE BRUYNE (Manchester City FC)

JORGINHO (Chelsea FC)

N’Golo KANTÉ (Chelsea FC)

UEFA ta fitar da ‘Yan kwallon Turai
Kevin De Bruyne, Jorginho da N'Golo Kante Hoto: www.skysports.com
Asali: UGC

Wanene zai zama Kocin shekara?

A rukunin masu horas da ‘yan wasa, ‘yan jaridar da suka shiga zabe a wannan karo su fito da sunayen masu horas da ‘yan kwallo uku a nahiyar Turai.

Thomas Tuchel (Chelsea)

Pep Guardiola (Manchester City)

Roberto Mancini (Italiya)

Kamar yadda UEFA ta bayyana a shafinta na yanar gizo a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, a rukunin kocin 'yan wasan kwallon kafa mata, an samu:

Lluís CORTÉS (FC Barcelona)

Peter GERHARDSSON (Sweden)

Emma HAYES (FC Women)

A wajen bikin da za ayi a Istanbul, za a fadi ‘yar wasar da ta fi kowa kokari a kakar wasan bana.

Ronaldo za su hadu da Messi?

Ku na da labari cewa Kungiyar PSG tana kokarin dauko Cristiano Ronaldo daga Juventus domin ya buga kwallo tare da Lionel Messi, Neymar Jr., da Sergio Ramos.

Rahotanni sun ce Kylian Mbappé yana so ya bar PSG, ya koma buga wasa a Real Madrid. Hakan zai bada dama a hada Ronaldo da tsohon gwarzon na Barcelona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel