Jerin ’Yan Wasan Najeriya 15 da Suka Fi Kwasar Makudan Kudi a Kungiyoyinsu

Jerin ’Yan Wasan Najeriya 15 da Suka Fi Kwasar Makudan Kudi a Kungiyoyinsu

Najeriya ta na da zakakuran matasan ‘yan wasa da suka yi fice a harkar kwallon kafa a duniya baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Daga cikin ‘yan wasan akwai wadanda ke buga wasa a gida da kuma kasashen Nahiyar Turai inda suke kwasar kudi, cewar Pulse.

'Yan wasan Najeriya 15 da suka fi kowa dibar makudan kudade a kungiyoyinsu
Kwallo: 'Yan wasan Najeriya da suka fi albashi Hoto: Samuel Chukwueze,Victor Osimhen, Alex Iwobi.
Asali: Twitter

Wannan rahoton zai kawo muku jerin ‘yan wasan Najeriya 15 da suka fi kowa dibar albashin makudan kudi a kungiyoyinsu.

Legit Hausa ta jero muku sunayen ‘yan wasan guda 15 da suka fi samun kudade:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wane 'yan kwallo suka fi samun albashi?

1. Victor Osimhen

Dan wasan da ke buga tamola a Napoli da ke Italiya shi ne yafi kowa samun kudi a cikin jerin 'yan wasan, cewar Africa Fact Zone.

Kara karanta wannan

“Maimakon farfado tattalin arziki, Gwamnan CBN ya kama hanyar jawo karin talauci”

Victor ya na samun akalla fan dubu 167 a ko wane mako wanda bajintarsa a yanzu ta saka kungiyoyi da dama ke zawarcinsa.

2. Samuel Chukwueze

Samuel shi ne na biyu a jerin masu kwasar kudi a Najeriya inda ya ke samun fan dubu 84,413 a mako.

Chukwueze ya na buga tambola ne a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ke kasar Italiya.

3. Alex Iwobi

Alex Iwobi wanda ke buga tambola a kungiyar Fulham ya na dibar kudade har fan dubu 80 a ko wane mako.

Iwobi ya sha suka daga bangarorin kasar bayan rashin bajinta musamman a wasan karshe na gasar AFCON.

4. Kelechi Iheanacho

Kelechi ya kasance na hudu a jerin mafi dibar kadaden inda ya ke samun fan dubu 80 a mako.

Dan wasan gaban na kungiyar Leicester City ya taka rawar gani a wasanni biyun karshe na gasar AFCON.

5. Wilfred Ndidi

Kara karanta wannan

Yan wasan ƙwallon ƙafa 5 da aka dakatar da su saboda sun yi amfani da ƙwayar ƙarin kuzari

'Dan wasan da ke buga wasa a Leicester City ya kasance na biyar inda ya ke samun fan dubu 75 a ko wane mako, Nigerian Queries ta tattaro.

Ndidi ya shigo kungiyar ne a shekarar 2016 wanda a yanzu ake ganin darajarsa a kasuwa ta kai fan miliyan 16.

Sauran 'yan wasa masu albashi

6. Joe Aribo - Southampton, fan dubu 70,000

7. Taiwo Awoniyi - Nottingham Forest, fan dubu 50,000

8. Paul Onuachu - Trabzonspor, fan dubu 47,511

9. Calvin Bassey - Fulham, fan dubu 47,000

10. Ola Aina - Nottingham Forest, fan dubu 40,000

11. Frank Onyeka - Brentford, fan dubu 40,000

12. Emmanuel Dennis - Nottingham Forest, fan dubu 40,000

13. Moses Simon - Nantes, fan dubu 39,492

14. Ademola Lookman - Atalanta, fan dubu 38,011

15. Victor Boniface - Bayer Leverkusen, fan dubu 32,819

An dakatar da Ronaldo daga wasa

Kara karanta wannan

Jerin ministocin Tinubu 12 da suka fi kowa kokari bayan binciken ayyukansu

Kun ji cewa Hukumar kwallon kafa ta Saudiyya ta dakatar da fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo.

Hukumar ta dakatar da dan wasan ne wasa daya saboda wani abu da ya yi da ke nuna rashin da'a a wasan da aka gabatar a karshen mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.