“Maimakon Farfado da Tattalin Arziki, Gwamnan CBN Ya Kama Hanyar Jawo Karin Talauci”

“Maimakon Farfado da Tattalin Arziki, Gwamnan CBN Ya Kama Hanyar Jawo Karin Talauci”

  • Kwamitin MPR a karkashin jagorancin shugabannin bankin CBN sun kara kason da za a rika karba a matsayin ruwa wajen cin bashi
  • Gwamnati tana kokarin magance hauhawar farashi da tsadar kaya, Peter Obi ya ce matakin da aka dauka ba zai iya kawo mafita ba
  • Peter Obi ya fadawa Bola Tinubu cewa idan bankuna suka fara daura ruwan 30% wajen bada bashi, adadin talakawa za su karu sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - An rahoto cewa kwamitin MPR mai kula da tsare-tsaren kudi a bankin CBN ya kara kason kudin ruwa a bankuna zuwa 22.5%.

A yayin da yake maida martani a game da wannan mataki da aka dauka, Peter Obi a shafin X ya nuna ba abin a shiga farin ciki ba ne.

Peter Obi da Bola Tinubu
Peter Obi ya soki manufofin CBN da Bola Tinubu a Najeriya Hoto: @PeterObi/@Dolusegun
Asali: Twitter

Matakan da aka dauka a gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Yadda aka damke shugabannin kamfanin Binance daga kasar waje a yunkurin karya Dala

‘Dan takaran shugabancin Najeriyan na LP a zaben 2023, ya ce karin ruwa a kan bashin banki zai haifar da karin matsala a tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin CBN ya bukaci bankunan kasuwa su rika ajiye akalla 45% na kudinsu a asusu, wannan zai rage adadin kudin da ke yawo a gari.

Peter Obi bai gamsu da wadannan matakai da aka fito da su a ranar Alhamis, kuma ya nuna sam ba za su magance matsalolin kasar ba.

Peter Obi da ilmin tattalin arziki

A bayaninsa, ‘dan kasuwan ya yarda shi ba kwararre ba ne ko masani a hakar tattalin arziki, amma ya ce ya san sha'anin kasuwanci.

"Ina da ra’ayi mai karfi cewa matakin kwamitin MPC na kara ruwa zuwa 22.5% da kason kudin da za a ajiye zuwa 45% zai kara munana halin tattalin arzikin mafi yawan gidaje,

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

"zai jawo rashin ayyukan yi musamman a bangaren kere-kere da wasu harkokin da suka dogara da bashin banki da karbar aro wajen samun kudin bukatunsu."

- Peter Obi

Peter Obi ya fadawa Tinubu mafita

A cewar ‘dan takaran na LP, tsuke kudi a kasuwa bai zai bunkasa tattalin arziki ba.

Musamman yanzu da ake da karancin da tsadar abinci, Peter Obi yana ganin tsarin da CBN ya fito da shi ba zai rage hauhawar farashi ba.

Obi ya yi ikirarin cewa 12% na N3.6tr da aka buga ne kurum a banki, ya ce N3.168tr yana kasuwa, amma yanzu za a janye takardun kudin.

A karshe tsohon gwamnan ya ce magance matsalar tsaro ne kurum zai sa a samu abinci.

Kano za iya tsere da Legas?

Ganin cigaban tattalin arzikin da aka samu, wasu sun fara kwadayin a fara aikin jiragen kasa a Kano kamar yadda ake gani a jihar Legas.

Bashir Ahmaad yana ganin aikin jirgin kasa ya fi muhimmanci a kan karo gadaje a Kano, wannan ce shawarar da ya ba Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel