Atiku da Obi Sun Aike da Sako Mai Muhimmanci Kan Rashin Nasarar Super Eagles a Wasan Karshe Na AFCON

Atiku da Obi Sun Aike da Sako Mai Muhimmanci Kan Rashin Nasarar Super Eagles a Wasan Karshe Na AFCON

  • Atiku Abubakar da Peter Obi sun mayar da martani daban-daban kan rashin nasarar Super Eagles a wasan ƙarshe na AFCON 2023
  • Ivory Coast ta doke Super Eagles ta Najeriya a ranar Lahadi a wasan ƙarshe na AFCON 2023, inda ta lashe gasar, Najeriya ta zo matsayi na biyu
  • Atiku da Obi sun dage cewa ƴan wasan Super Eagles sun yi iya ƙoƙarinsu ko da kuwa ba su samu damar zama zakaru ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam'iyyar LP, Peter Obi sun yabawa Super Eagles bisa rawar da suka taka a wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun shiga jimamin rashin da Super Eagles ta yi a wasan AFCON 2023, ga martaninsu

Ku tuna cewa Ivory Coast ta lashe gasar AFCON 2023 bayan ta doke Najeriya da ci 2-1 a filin wasa na Alassane Ouattara a daren ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Atiku da Obi sun yabi 'yan wasan Super Eagles
Atiku da Obi sun yaba da kokarin Super Eagles a wasan karshe na AFCON Hoto: @atiku, @PeterObi, @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Ivory Coast ce ta karɓi baƙuncin gasar karo na 34, kuma Legit Hausa ta sanya ido kan yadda wasan ƙarshen ya kaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Atiku da Peter Obi Suka Ce?

Da yake mayar da martani ta hanyar wani rubutu a shafinsa na X, Atiku ya ce wannan ba shine sakamakon da ake tsammani ba, amma Super Eagles sun yi iya ƙoƙarinsu.

Atiku ya rubuta cewa:

"Ba sakamakon da muka yi tsammani ba. Duk da haka, muna ci gaba da kasancewa #SuperEagles. Har yanzu muna alfahari da ku. Da kyau, @NGSuperEagles. -AA"

Hakazalika, Obi ya yi amfani da shafinsa na X inda ya yaba wa Eagles bisa jajircewar da suka nuna lokacin wasan, inda ya ce sun yi ƙwazo sosai kuma dama wasa ya gaji haka.

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Malamin da ya yi hasashen nasarar Tinubu, ya yi magana kan Osimhen

Obi ya rubuta cewa:

"A wasanmu na ƙarshe da ƴan uwanmu na Afirika, Cote d’Ivoire, a yau, mun zo ƙarshen gasar AFCON, ƴan wasanmu na ƙasa Super Eagles sun yi iya ƙoƙarinsu da ƙarfin gwiwa, jajircewa, da dabaru, amma a ƙarshe, Cote d'Ivoire ta yi nasara, ta kuma lashe kofin.
"Ina taya ƴan wasan ƙasarmu, da kuma duk wani ɗan Najeriya murnar baje kolin hazaƙa da fasahar ƙwallon ƙafa wanda ya sa mu ka yi nisa a gasar.

Tinubu Ya Yabi Super Eagles

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da ƙwazon da ƴan wasan Super Eagles suka nuna a wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023.

Shugaban ƙasan ya yaba ɗa jajircewar da ƴan wasan suka nuna duk kuwa da rashin nasarar da suka yi a hannun Ivory Coast, masu masaukin baƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel