AFCON: Ni Ba Iwobi Ba Ne, Sadiq Umar Ya Dira Kan ’Yan Najeriya da Ke Sukarsu Bayan Rashin Nasara

AFCON: Ni Ba Iwobi Ba Ne, Sadiq Umar Ya Dira Kan ’Yan Najeriya da Ke Sukarsu Bayan Rashin Nasara

  • Yayin da Alex Iwobi ya shiga kunci bayan sukar da ya ke sha a wurin ‘yan Najeriya, Sadiq Umar ya ce shi babu wanda ya isa
  • Dan wasan gaban Super Eagles ya koka kan yadda aka sako Iwobi a gaba inda ya ce babu wanda ya isa ya masa haka
  • Sadiq na magana ne bayan sukar wasu ‘yan wasan Super Eagles da aka yi bayan rashin nasararsu a gasar AFCON

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Dan wasan gaban Super Eagles, Sadiq Umar ya yi martani kan caccakar Alex Iwobi da ake yi a kafafen sadarwa.

Sadiq na magana ne bayan sukar wasu ‘yan wasan Super Eagles da aka yi bayan rashin nasararsu a gasar AFCON.

Kara karanta wannan

Hadimin Ganduje yayi tonon asiri, ya nemi Abba ya dawo da Sanusi, a tsige Sarakuna 5

Sadiq Umar ya gargadi masu sukarsu kan rashin nasara a gasar AFCON
Sadiq ya ce shi ba Iwobi ba ne, ba zai dauki hakan ba. Hoto: @sadiq_umar19, @ng_supereagles.
Asali: Instagram

Mene Sadiq ke cewa kan 'yan Najeriya?

Iwobi ya sha suka sosai saboda rawar da ya taka wacce ake ganin ta jawo rashin nasarar Super Eagles a wasan karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Sadiq shi ma ya sha sukar duk da rashin kasancearsa a gasar baki daya saboda rauni da ya samu tun farko.

Sai dai Sadiq sabanin Iwobi wanda ya goge dukkan wallafawarsa a kafofin sadarwa ya yi martani mai zafi kan masu sukar tasa.

Umar ya wallafa a shafin Instastories inda ya gargadi masu sukar da kada su kai shi bango don shi ba Iwobi ba ne.

Martanin Sadiq Umar kan AFCON

Dan wasan ya kuma soki masu caccakar Iwobi kamar yadda ya rubuta:

“Ko buga wasa ban yi ba kuna zagi na, ku yi hakuri ni ba Iwobi ba ne, zan ci mutuncin mutum hade da babansa da mamansa gaba daya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun shiga jimamin rashin da Super Eagles ta yi a wasan AFCON 2023, ga martaninsu

“Ni asalin Bahaushe ne ba na tsoron komai ku duba idona, kuna tura mutum bango har ya samu matsalar damuwa da na kwakwalwa.
“Kuma a hakan kuna son rayuwa ta yi muku kyau kuma, baku isa ba, marasa abin yi.”

Wannan na zuwa ne bayan Sadiq ya koma kungiyarsa ta Real Sociedad bayan samun rauni tun kafin fara gasar AFCON.

Musa ya yi magana kan makomarsa

A baya, kun ji cewa Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya yi magana kan makomarsa bayan kammala gasar AFCON.

Musa ya ce har yanzu shi dan wasa ne don haka duk lokacin da ake bukatarsa a tawagar zai amsa gayyata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel