Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da Wasu ‘Yan Najeriya 4 da Suka Kwanta Dama Yayin Gasar AFCON

Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da Wasu ‘Yan Najeriya 4 da Suka Kwanta Dama Yayin Gasar AFCON

A ranar Laraba 7 ga watan Faburairu ne aka fafata tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023 a birnin Bouake.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A yayin wasan, 'yan Najeriya sun kasance cike kwarin gwiwa tare da hasashen kasar ce za ta samu nasara.

Wasan, wanda aka kare shi a 1-1 bayan karin lokaci da aka yi, ya sa an kai ga bayar da fenariti kuma hakan ya yi sanadiyar rasa rayukan wasu 'yan Najeriya biyar saboda zullumi.

'Yan Najeriya 5 ne suka mutu yayin karo tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu
Najeriya vs Afrika ta Kudu: Jigon APC da Wasu ‘Yan Najeriya 4 da Suka Kwanta Dama Yayin Wasan Hoto: @UnlimitedEniola
Asali: Twitter

A lokacin wasan, kungiyar Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana na Afrika ta Kudu duk sun ci kwallonsu ne ta hanyar fenariti.

Kara karanta wannan

AFCON: Tsohon hadimin Buhari ya tuna arangamarsa da wani 'dan Obidient a wasan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

William Troost-Ekong, kyaftin din Najeriya, ya zurawa Super Eagles kwallo a cikin raga a mintuna 67, yayin da Teboho Mokoena na Bafana Bafana shima ya zurawa Afrika ta Kudu kwallo a raga cikin mintuna 90.

An tabbatar da mutuwar akalla 'yan Najeriya biyar a yayin buga fenariti. Ga jerinsu a kasa:

1. Cairo Ojougboh

Cairo Ojougboh, jigo na jam'iyyar APC kuma tsohon 'dan majalisar wakilai, wanda ya wakilci mazabar tarayya ta Ika, jihar Delta, ya mutu yayin da aka bayar da fenariti kan Najeriya.

Majiya ta ce:

"Ya yanke jiki ya fadi a lokacin da aka bayar da fenariti akan Najeriyan yayin gasar AFCON da Kudu ta Afrika a wasan kusa da karshe da aka yi a ranar Laraba a Bouake, Ivory Coast."

2. Alhaji Ayuba Abdullahi

Mataimakin Bursar na jami’ar jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a daren Laraba a lokacin da yake kallon wasan kusa da karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.

Kara karanta wannan

AFCON: Fitaccen ɗan kasuwa ya mutu yana tsaka da kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

An rahoto cewa Abdullahi ya fara jin babu dadi ne a lokacin da yake kallon wasan a wata cibiyar wasanni da ke unguwar Sango a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, kuma daga karshe ya mutu.

3. Dan bautar kasa Samuel

Wani mummunan al'amari da ya sake faruwa a yayin wasan kusa da karshe na AFCON shine mutuwar wani dan bautar kasa wanda aka bayyana a matsayin Samuel.

An rahoto cewa Samuel, wanda ya fito daga jihar Kadunayana yin bautar kasarsa ne a Adamawa, lokacin da ya mutu.

An tattaro cewa ya mutu ne a lokacin fenariti. Kamar yadda jarin Punch ta rahoto, shugaban NYSC a jihar Adamawa, Jingi Dennis ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu.

Dennis ya ce an tabbatar da mutuwar Samuel ne a babban asibitin Numan.

4. Mikhail Osundiji

Osundiji yana cikin 'yan Najeriya da suka mutu yayin kallon wasan kusa da karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Kara karanta wannan

AFCON: Kada ka kuskura ka dawo kasarmu, 'yan Afirka ta Kudu sun gargadi dan Najeriya, sun yi bayani

An rahoto cewa marigayin ma'aikaci ne a kamfanin Nestle.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Osundaji ya yanke ciki ya fadi sannan ya mutu saboda kaduwa lokacin da alkalin wasa ya soke kwallo na biyu da Victor Osimhen ya ci wa Najeriya.

5. Osondu Nwoye

Attajirin 'dan kasuwan Najeriya, Cif Osondu Nwoye, ya kwanta dama a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu, 2024.

Fitaccen ɗan kasuwar ya mutu ne yayin da yake kallon karawar tawagar Super Eagles a wasan dab da na ƙarshe da Afirka ta Kudu.

Tawagar Super Eagles sun yi wa wadanda suka mutu addu'a

A gefe guda, mun ji cewa tawagar Super Eagles ta yi addu'a na musamman ga wadanda suka rasa ransu yayin kallon wasanta da Afirka ta Kudu.

Idan ba a manta ba, a jiya Alhamis 8 ga watan Faburairu an sanar da mutuwar mutane biyar da suka rasa ransu dalilin wasan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng