AFCON: Fitaccen Ɗan Kasuwa Ya Mutu Yana Tsaka da Kallon Wasan Najeriya da Afirka Ta Kudu

AFCON: Fitaccen Ɗan Kasuwa Ya Mutu Yana Tsaka da Kallon Wasan Najeriya da Afirka Ta Kudu

  • Cif Osondu Nwoye ya rasu a filin wasan da Super Eagles ta ɓarje gumi da tawagar Bafana Bafana ta ƙasar Afrika ta Kudu
  • Rahotanni sun nuna cewa fitaccen ɗan kasuwan ya yanke jiki ya faɗi ne tun a filin wasan Stade de la Paix in Bouaké, Côte d’Ivoire
  • Ganau sun bayyana cewa marigayin ya yi murna tare da ƙara mai karfi da muryarsa lokacin da Osimhen ya zura kwallo ta biyu wacce VAR ta kashe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bouaké, Ivory Coast - Wani dan kasuwan Najeriya, Cif Osondu Nwoye, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu, 2024.

Fitaccen ɗan kasuwar ya mutu ne yayin da yake kallon karawar tawagar Super Eagles a wasan dab da na ƙarshe da Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

AFCON: Tsohon hadimin Buhari ya tuna arangamarsa da wani 'dan Obidient a wasan Najeriya

Tawagar Super Eagles.
AFCON: Fitaccen Attajiri Ɗan Anambra Ya Mutu a Filin Wasan Najeriya da South Africa Hoto: MB Media/Getty Images
Asali: Getty Images

Wani mai suna, Chukwudi Iwuchukwu, shi ne ya sanar da mutuwar Cif Osondu a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda Sahara Reporters ta tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare guda, Najeriya ta lallasa Afirka ta Kudu da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da suka tashi 1-1 cikin mintuna 120.

Yadda ɗan kasuwan ya sume ana cikin wasa

Amma rahotanni sun ce Mista Osondu ya mutu ne a yayin da ake tsaka da murza leda a wasan kuma kafin cikar mintuna 90.

A cewar wanda ya tabbatar da rasuwar a Facebook, ɗan kasuwan wanda ya fito daga jihar Anambra, ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da alkalin wasan ya soke kwallo ta biyu.

Ya ce mutumin ya faɗi ƙasa ne bayan alkalin da ke jagorantar wasan ya soke kwallo ta biyu da Super Eagles ta ci.

Kara karanta wannan

Babban jigon APC ya yanke jiki ya mutu yayin da ya ke kallon wasan Najeriya

An yi kokarin ceto rayuwarsa?

Sai dai duk ƙoƙarin da aka yi domin ceto rayuwarsa ya ci tura inda daga ƙarshe likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa a Asibiti.

“Ya je Bourke, birnin da ya karbi bakuncin Super Eagles a jiya, domin kallon wasan Najeriya. Yana son kwallon kafa kuma yana kishin kasarsa.
"Wataƙila kaɗuwar soke ƙwallo ta biyu da kuma bai wa South Africa bugun fenarati ne ya yi wa zuciyarsa nauyi, wanda ya yanke jiki ya faɗi a filin wasan."

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu

A wani rahoton kuma Alhaji Ayuba Abdullahi, mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara ya kwanta dama a yayin da yake kallon kwallon Najeriya da Afrika ta Kudu

An ruwaito cewa hawan jinin Abdullahi ne ya tashi ana daf da kammala buga wasan, inda ya yanke jiki ya fadi aka garzaya da shi asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel