AFCON: Ahmed Musa Ya Jagoranci Super Eagles Wurin Addu'a Ga Wadanda Suka Mutu, Ya Dauki Alkawari

AFCON: Ahmed Musa Ya Jagoranci Super Eagles Wurin Addu'a Ga Wadanda Suka Mutu, Ya Dauki Alkawari

  • Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya jagoranci addu'ar jajantawa wadanda suka rasa ransu yayin kallon kwallo
  • A jiya ne aka samu rahoton mutuwar wasu mutane biyar a Najeriya sanadin kallon kwallon Najeriya da Afirka ta Kudu
  • Musa yayin addu'ar ya yi alkawarin cewa da yardar Allah za su dawo da kofin gida Najeriya ga wadanda suka mutu da sauran 'yan Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ivory coast - Tawagar Super Eagles ta yi addu'a na musamman ga wadanda suka rasa ransu yayin kallon wasanta da Afirka ta Kudu.

Idan ba a manta ba, a jiya Alhamis 8 ga watan Faburairu an sanar da mutuwar mutane biyar da suka rasa ransu dalilin wasan.

Kara karanta wannan

AFCON: Tsohon hadimin Buhari ya tuna arangamarsa da wani 'dan Obidient a wasan Najeriya

Super Eagles ta yi addu'a ga wadanda suka rasa ransu a ranar Laraba
Ahmed Musa ya jagoranci addu'a ta musamman ga wadanda suka mutu. Hoto: @ng_supereagles.
Asali: Instagram

Waye ya jagoranci tawagar Super Eagles a addu'ar?

Kyaftin din tawagar, Ahmed Musa shi ya jagoranci addu'ar inda suka yi wa 'yan Najeriya alkawarin dawo da kofin gida don wadanda suka mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo, Ahmed Musa ya yi magana tare da jimamin rasuwar yayin 'yan wasa da kwaca-kwacai ke tsaye kan kafafunsu.

A cewarsa:

"A jiya mun rasa 'yan Najeriya guda hudu dalilin wannan wasa, don haka za mu yi shiru na minti daya saboda su.
"Muna jajantawa iyalansu, duk da babu wani abu da za mu iya yi amma In shaa Allah a ranar Lahadi za mu dawo da kofin gida."

Kalli bidiyon a kasa:

Idan ba a manta ba a jiya ne aka sanar da mutuwar wasu 'yan Najeriya har guda biyar sanadin kallon wasan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

Bayan rasuwar jigon APC an samu matashi mai bautar kasa da wani Lakcara da kuma dan kasuwa a Anambra sai kuma wani magidanci a Ogun.

Nwabali na fuskantar barazana

Kun ji cewa 'yan kasar Afirka ta Kudu na yin barazana ga golan Najeriya, Stanley Nwabali.

Nwabali ya samu barazanar ce bayan Najeriya ta lallasa Afirka ta Kudu a sami fainal na gasar AFCON.

Golan ya na buga wasa ne a wata kungiyar kwallon kafa da ke kasar Afirka ta Kudu, Chippa United.

Asali: Legit.ng

Online view pixel