Ronaldo ya raba gardamar Ballon d’Or, ya bayyana wanda ya dace da kyautar bana

Ronaldo ya raba gardamar Ballon d’Or, ya bayyana wanda ya dace da kyautar bana

  • Ronaldo Delima yace Karim Benzema ya dace da Ballon d'Or a shekarar nan
  • Tsohon Tauraron Brazil yace Benzema ya cancanci ya zama gwarzon Duniya
  • Lionel Messi na PSG da Tauraron Man United, C. Ronaldo suna cikin takarar

Ronaldo Delima ya yi magana game da takarar kyautar Ballon d'Or na wannan shekara. Tsohon ‘dan wasan ya fadi wanda ya dace ya lashe gagarumar kyautar.

Daily Mail ta rahoto Delima yana cewa Karim Benzema ne ‘dan wasan da ya fi dace wa da kyautar, har yana ganin yana gaba da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.

Ganin ya yi nasara a gasar cin kofin nahiyar kudancin Amurka, wasu na ganin sabon ‘dan wasan Paris Saint-Germain, Lionel Messi ya cancanta ya ci kyautar.

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Amma shi tsohon tauraron na kasar Brazil yana so Benzema ne ya ci wannan kyauta, a cewarsa shi ne ya fi dace wa saboda icen da ya yi a shekarun bayan nan.

Benzema, ko shakka babu

Jaridar Marca ta ce da aka tambayi tsohon ‘dan wasan na Real Madrid, game da ra’ayinsa, sai yace Benzema.

Ronaldo, Benz
Karim Benzema da Cristiano Ronaldo a Euro Hoto: www.nevermanagealone.com
Source: UGC

“Babu tantama, ‘dan takara na Ballon d'Or shi ne Benzema.”
“Dan wasan gaban da ya fi kowa a Duniya, ya yi shekaru 10 yana tashe. Baya ga haka gwarzo. Ya cancanci kyauta. Ko ya kuke gani? - De Lima, Ronaldo.

Takarar Ballon D'or 2021

A Oktoban nan Benzema ya taimaka wa kasarsa ta Faransa wajen cin gasar UEFA Nations league. A gasar La-ligan 2021/22 kuwa, har ‘dan wasan ya ci kwallaye 9.

Read also

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

Irinsu Cristiano Ronaldo, N'Golo Kante da Robert Lewandowski suna cikin wadanda ke gaban a wajen neman cin wannan kyauta ta gwazon ‘dan kwallon shekara.

Kevin De Bruyne, Luis Suarez, Harry Kane da Kante duk suna cikin wadanda za su iya lashe kyautar.

Thibaut Courtois ya dura kan manya

Kwanakin baya ne Thibaut Courtois ya yi kaca-kaca da kungiyoin FIFA da UEFA bayan an kallama gasar Nations league da kasar Faransa ta samu nasara.

Courtois mai tsare ragar kungiyar Real Madrid da kasar Belgium yace an fi maida hankali a kan kudin da za a samu, a maimakon lafiya da walwalar ‘yan kwallo.

Source: Legit

Online view pixel