Albashin ma'aikata
Gwamnan jihar Kebbi, Kwamred Nasir Idris ya ce a shirye yake domin biyan mafi karancin albashi da duk aka amince da shi komai yawansa ga ma'aikata.
Tsohon Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ya ce ma’aikatan Najeriya na bukatar gwamnati ta biya su albashin da zai isa su gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Gwamnatin tarayya ta dage kan cewa ba za ta taba iya biyan abin da yah aura N62,000 ga ma’aikatan kasar nan ba duk da cewa ita ma kungiyar kwadago ta ja daga.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya raba kyautar N10,000 ga dukkan ma'aikatan jihar domin gudanar da bukukuwan sallar cikin walwala a jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya cika alƙawarin da ya ɗauka na fara biyan mafi ƙaracin albashi N30,000 ga ma'aikatan jihar, ya ce su yi shagalin Babbar Sallah cikin farin ciki.
Majalisar Tarayya ta tabbatar da shirinta na samar da dokar da za ta tilasta gwamnoni 36 a Najeriya da ma'aikatu masu zaman kansu biyan mafi karancin albashi.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya umarci ma'aikatar kuɗi da ta kananan hukumomi su biya albashin watan Yuni, 2024 gabanin ranar Babbar Sallah.
Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya ce gwamnatin tarayya da na jihohi za su iya biyan mafi karancin albash idan aka yi amfani kudin sata da aka kwato.
Kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) ta ce kananan hukumomin kasar nan ba za su iya biyan mafi karancin albashin da kungiyar kwadago ke nema ba.
Albashin ma'aikata
Samu kari