Abin da Zai Faru Nan Gaba Idan Gwamnati ta Karya Alkawarinmu Inji ‘Yan Kwadago

Abin da Zai Faru Nan Gaba Idan Gwamnati ta Karya Alkawarinmu Inji ‘Yan Kwadago

  • Kungiyar kwadago watau NLC ta yi karin-haske game da yajin-aikin da aka fasa shiga a makon nan
  • Kwamred Joe Ajaero ya nusar da gwamnatin tarayya cewa ba za su amince da rashin cika alkawari ba
  • Shugaban na NLC ya ce nan da kwanaki 30 za su waiwayi duk alkawuran da gwamnati ta dauka

Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC, ta ja-kunnen gwamnatin tarayya cewa nan gaba ba za ta bada sanarwar shiga yajin-aiki ba.

Idan har kwanaki 30 su ka wuce ba tare da an cika alkawuran da aka dauka ba, This Day ta rahoto cewa NLC za ta mamayi gwamnatin Najeriya.

Da aka yi hira da shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero, ya shaida cewa tsawon wata guda da su ka bada ya ishi gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir

‘Yan Kwadago
Zanga-zangar NLC Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yajin-aiki: Joe Ajaero ya yi magana

A cikin wannan lokaci, Joe Ajaero ya na ganin shugaban kasa zai iya kawo sauki kan halin kuncin tattalin arziki da ya ce al’umma sun shiga ciki..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi tunanin za a tafi yajin-aiki, kwatsam sai aka ji shugabannin kwadago sun sasanta da gwamnati, ma'aikata su ka koma bakin aiki a ko ina.

Meyasa NLC ta fasa tafiya yajin-aiki

A hirar da ya yi da tashar Arise, Ajaero ya bayyana cewa sun yarda su tattauna da gwamnati ne saboda yadda ‘yan Najeriya su ka huro masu wuta.

Shugaban na NLC ya ce wasu sun nuna masu mummunan tasirin da yajin-aiki zai yi musamman ga marasa karfi, saboda haka ne su ka canza tunani.

..NLC ba ta janye yajin aiki ba

"Idan a karshen wata gudan, ba mu gamsu da abubuwan da aka sa hannu a kansu ba, za mu sake komawa ‘ya 'yanmu, sai mu samu sabuwar dama.

Kara karanta wannan

NLC da TUC Sun Fasa Yajin-Aiki, Kungiya Ta Umarci Ma’aikatanta Su Tafi Ofis a Yau

Ya kamata mu fahimci abin da aka dakatar da shi ba za a kira shi wanda aka fasa ba.
Ba za mu ba gwamnati sabon wa’adi ba. Za mu koma mu duba nasarorin da mu ka samu da yanayin hobbasan da aka yi wajen cin cika alkawari."

- Joe Ajaero

Yarjejeniyar da aka yi da NLC &TUC

Ana da labari an yi karin N35, 000 a albashin ma’aikata kuma za ayi kokarin rage farashin dizil tare da duba albashin malaman jami’o’in gwamnati.

Idan da gaske gwamnati mai-ci ta ke yi, zuwa yanzu Kwamred Ajaero ya na ganin ya kamata an samar da motoci masu amfani da CNG a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng