‘Yan Majalisa Sun Hana a Yafewa Talaka Biyan NECO, UTME, WAEC Saboda Tsadar Rayuwa

‘Yan Majalisa Sun Hana a Yafewa Talaka Biyan NECO, UTME, WAEC Saboda Tsadar Rayuwa

  • Majalisar wakilan tarayya ta ki karbar kudirin da aka gabatar da zai tilastawa gwamnati kin karbar kudin jarrabawar SSCE
  • Anamero Dekeri ya so ayi wa marasa hali afuwar biyan NECO, JAMB da UTME saboda tsadar rayuwa a dalilin tashin fetur
  • ‘Yan majalisa da-dama sun yi kaca-kaca da kudirin Hon. Anamero Dekeri, a karshe bai je ko ina ba da aka yi muhawara

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da wani kudiri da ya nemi a hakura da karbar kudin jarrabawar SSCE na shekarun 2023 da 2024.

Hon. Anamero Dekeri (APC Edo) ya kawo wannan kudiri a majalisar tarayya domin a saukakawa jama’a, rahoton ya fito ne a jaridar The Cable.

Bayan muhawarar da aka tafka a zauren, ‘yan majalisar wakilai ba su yi na’am da hakan ba.

Kara karanta wannan

Za a Binciki N11.3tr da Buhari da Jonathan su ka kashe a Matatu Daga 2010-2023

‘Yan Majalisa
Majalisar Wakilai ta ki yafe kudin UTME, NECO da WAEC Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Hon. Dekeri ya nemi a yafe kudin SSCE

Da Hon. Anamero Dekeri ya yi nasara, dalibai ba za su biya kudin jarrabawowin WAEC, NECO da UTME da ake yi bayan gama sakandare ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar na jihar Edo ya ce a sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, rayuwa ta yi mutanen kasar tsada musamman marasa karfi.

A cewar Dekeri, wasu mugaye su na amfani da wannan dama domin kara azabtar da jama’a yayin da talakawa su ke kukan rayuwa ta kara tsada.

Talaka zai iya biyan SSCE a yau?

Daga cikin abin da ‘dan majalisar tarayyan yake gani zai taimaki masu karamin karfi shi ne dawainiyar ilmin ‘ya ‘yansu kamar kudin jarrabawa.

Rahoton ya ce saboda haka Dekeri ya nemi a yafe karbar kudin WAEC, NECO da UTME daga hannun marasa hali a shekarar bana da badi.

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kunno a APC, Ana Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisar Tarayya

'Yan majalisa sun ce ba za su yarda ba

A tashin farko, shugaban masu rinjaye, Julius Ihonvbere ya nuna rashin goyon bayansa, ya ce kowane ‘dan majalisa ya dauki nauyin mutanensa.

Premium Times ta rahoto Alhassan Ado Doguwa ya na cewa ko a yanzu wasunsu su na biyan wadannan kudi, a cewarsa aikin ‘yan majalisar kas ne.

Da Abbas Tajudeen ya nemi a kada kuri’a, mafi yawan ‘yan majalisar ba su karbi kudirin ba.

Za a kawo kasafin 2024 a Nuwamba - Majalisa

Ana da labarin cewa Majalisar Dattawa ta ce za ta yi aiki da kyau a kasafin kudi domin talaka ya amfana da kudin da za a batar a shekarar 2024

A mako mai zuwa ne takardar MTEF za ta je gaban sanatoci, zuwa karshen Nuwamba kuma Bola Tinubu zai gabatar da kundin kasafin badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel