Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Kungiyar NLC Kan Shirinsu Na Shiga Yajin Aiki A Fadin Kasar

Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci Kungiyar NLC Kan Shirinsu Na Shiga Yajin Aiki A Fadin Kasar

  • Gwamnatin Tarayya ta shirya wata ganawa ta musamman da Kungiyar Kwadago ta NLC, don tattaunawa kan yajin aiki
  • Ministan Kwadago da Ayyuka, Simon Lalong shi ya shirya wannan gayyatar ga kungiyar don dakile shirin shiga yajin aiki
  • Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Olajide Oshundun shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 17 ga watan Satumba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Ministan Kwadago da Ayyuka, Simon Lalong ya gayyaci Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) wata ganawa don dakile shirinsu na shiga yajin aiki.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Olajide Oshundun shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 17 ga watann Satumba.

FG ta gayyaci kungiyar NLC don tattaunawa
Gwamnatin Tarayya Za Ta Gana Da Kungiyar NLC Kan Yajin Aiki. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye dalilin gayyatar NLC don tattaunawa?

Ministan ya umarci bangaren kasuwanci da ma’aikatu a karkashinsa da su hada musu ganawa da kungiyar NLC don tattaunawa kan matsalolin, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shara ta kare a Kano, Abba Gida-Gida ya dauki ma'aikatan tsaftace birni mutum 4500

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya na da muhimmanci zaman da kungiyar za ta yi da gwamnati don kawo karshen matsalolin da ke tsakani da kuma dakile kawo cikas ga tattalin arziki.

Lalong ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta ci gaba da tattaunawa da NLC bayan shawarwari da ta yi don tabbatar da an samu daidaito a ma’aikatu da kuma samun kudin shiga, cewar Channels TV.

Sau nawa aka gayyaci NLC tattaunawa?

Idan ba a mantaba, ministan a baya ya gayyaci kungiyar don tattaunawa a kokarinsu na shiga yajin aikin kwanaki biyu a ranar 5 zuwa 6 ga watan Satumba.

Amma kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC ce kadai ta samu damar halartar ganawar yayin da kungiyar NLC ta kaddamar da yajin aikin gargadin na kwanaki biyu.

Kungiyar dai na fafutukar ganin 'yan Najeriya sun samu sauki musamman dalilin cire tallafi da gwamnatin ta yi.

Kara karanta wannan

"Ba Minista Ne Kawai Ba", Tinubu Ya Bayyana Matsayin Wike A Zuciyarsa, Ya Yi Bayani

Kungiyar NLC ta janye yajin aikin kwanaki 2

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ta yi daga ranar 5 zuwa 6 ga watan Satumba.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka inda ya ce an samu biyan bukata.

Ya kuma umarci ma’aikata da su koma bakin aiki a washe gari inda ya musu godiya da irin goyon baya da suka bai wa kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.