Siyasar Najeriya
Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyan Najeriya ya ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya umarci yan sandan jiharsa su kama ɗan majalisar wakilan tarayya duk inda suka ganshi bisa zargin hayar yan daba da kai hari.
Hukumar NDLEA ta tura wasika ga shugaban jam'iyyar APC, ta nemi a fara yiwa 'yan takara daga jam'iyyar APC gwajin shan kwaya gabanin zaben fidda gwani da za ayi
Wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban tsagin APC a jihar Bayelsa Sunday Frank-Oputu. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da ya kalubalanci APC a jihar.
Kungiyar dattawan arewa ta bayyana cewa ba a taba samun baraka a cikin ta ba domin mambobinta na biyayya ga Farfesa Ango Abdullahi a matsayinsa na shugabansu.
Tun bayan zartar da sabon kundin zaɓen 2022, da yawan masu niyyar tsayawa takara na bin doka wajen aje aikinsu domin neman wata kujeea, haka ta faru a Sokoto.
A yau Sanatan APC ya kawo karshen rade-radi, ya ayyana burin neman Shugaban kasa. Yanzu Sanatoci 3 sun ayyana burin tsayawa takara Shugaban kasa a zaben badi.
Majalisar dokokin Adamawa ta ayyana kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Michika, Joseph Ayuba, a matsayin babu kowa kan sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Gwamnan jihar Ekiti ya ce watakila ya shiga takarar Shugaban kasa. Kayode Fayemi ya ce irinsa ake nema a Aso Villa wanda ya san aiki, yake da ilmi da jajircewa.
Siyasar Najeriya
Samu kari