Tashin hankali: An ji muryar wani dan majalisar tarayya na PDP na barazanar kashe wani

Tashin hankali: An ji muryar wani dan majalisar tarayya na PDP na barazanar kashe wani

  • An ji Gboluga Dele Ikengboju a wani faifan sauti yana barazanar kashe wani mutum a kan wasu wakilan jam'iyya
  • Ikengboju shine dan majalisa mai wakiltar mazabar Okitipupa/Irele a jihar Ondo a majalisar dokokin tarayya
  • Dan majalisar ya sha alwashin kashe wani jigon PDP, Elder Amos Fadope kan jerin sunayen wakilan jam’iyyar

An ji dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Okitipupa/Irele a jihar Ondo a majalisar wakilai ta kasa, Hon Gboluga Dele Ikengboju, a wani faifan sauti yana barazanar halaka wani mutum.

A cikin wani faifan sautin, dan majalisar a lokacin da ke waya da Elder Amos Fadope, ya caccaki jigon na jam’iyyar PDP kan wani dan jam’iyyar da aka zaba a matsayin wakili.

Sautin dan majalisa na barazanar kashe wani
Tashin hankali: An ji muryar wani dan majalisar tarayya na PDP na barazanar kashe wani | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Dan majalisar wanda ya kira Fadope sunaye daban-daban bakake a cikin faifan sautin ya yi alwashin halaka shi.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Da yake magana kan lamarin, Niyi Arogbo, wanda kansa ake barazanar, ya yi ikirarin cewa dan majalisar ya gaza a yunkurinsa na cire shi daga jerin sunayen wakilan jam’iyyar ne, don haka ya yi amfani da kalamai mara dadi ga jigon jam’iyyar.

Yace:

“Guraben wakilan an tura su ne zuwa yankina, kuma jama’ata baki daya sun tsayar da ni a matsayin shugaban gundumar kuma shugaban gundumar ya san wanda na zaba bai yi masa ba sai ya yanke shawarar raina min hankali ta hanyar zabar wanda ba mu so.

Yayin da Legit.ng ta tuntubi dan majalisar, ya ki mai da martani kan lamarin, inda yace sam bai da ta cewa akai.

Saurari sautin:

2023: Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

A wani labarin, tsohon kakakin majalisar wakilai, Honorabul Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Bankole ya shirya lale miliyan N100m domin sayen Fom karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.

Wani makusancin tsohon kakakin majalisar wakilan, Malam Abdullahi Bayero, shi ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel