2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC

2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC

  • Babbar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) na yin duk mai yiwuwa don ganin ta kafa kanta sosai kafin zaben 2023
  • A yanzu haka, tsoffin ministocin jam’iyyar adawar sun fara aiki domin karfafa hadin kan jam’iyyar tare da shirin kwato mulki daga hannun APC
  • Hakazalika, ministocin sun amince da sanya idanu sosai a wajen tantance yan takarar PDP domin tabbatar da ganin an tsayar da wadanda suka cancanta

Abuja Tsoffin ministocin da suka yi aiki a karkashin inuwar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na aiki domin tabbatar da ganin cewa an tsayar da yan takarar da suka cancanta don fuskantar APC a babban zaben 2023.

A yanzu haka, tsoffin ministocin sun zuba idanu sosai kan tsarin tantance dukkanin yan takarar shugaban kasa na PDP, AIT News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC
2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC Hoto: PDP
Asali: UGC

Rahoton ya kuma kawo cewa an cimma wannan matsayar ne a wata ganawa da suka yi a daren ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, a Abuja duk daga cikin kokarin sanin dukkanin masu neman takarar shugaban kasa da cancantarsu wajen samar da shugabanci nagari.

Sun kuma nuna damuwa game da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa da kuma tabarbarewar tattalin arziki da ‘yan Najeriya da dama ke fama da su.

Har ila yau, tsoffin mambobin majalisar zartarwar a karkashin gwamnatin PDP sun yanke shawarar aiki tare da dukkanin yan takara domin karfafa hadin kan jam’iyyar.

Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa

A wani labarin, mun ji cewa wani dan majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Oluwole Ogunmolasuyi, ya gamu da fushin al’ummar mazabarsa inda suka kai masa farmaki kan zargin rashin yi masu aiki.

Kara karanta wannan

Rochas Okorocha da wasu Sanatoci 3 da za su yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Ogunmolasuyi ya kasance dan majalisa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltan mazabar Owo 1 kuma shine shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin na jihar Ondo.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Tosin Fapohunda II, ne ya wallafa bidiyo wanda a ciki ne aka farmaki dan majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel