Babu baraka a kungiyar dattawan arewa, muna biyayya ga Ango Abdullahi – Baba Ahmed

Babu baraka a kungiyar dattawan arewa, muna biyayya ga Ango Abdullahi – Baba Ahmed

  • Kungiyar dattawan Arewa ta NEF ta bayyana cewa babu kowani baraka da ya kunno kai a cikin gidanta
  • Kakakin kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa su masu biyayya ne ga shugabansu, Farfesa Abdullahi Ango
  • Hakan martani ne ga cece-kucen da ya biyo bayan sanarwar da ya fitar game da matsayar kungiyar a kan batun maslaha a PDP

Kaduna - Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa ba a taba samun baraka a cikin kungiyar ba domin mambobinta na biyayya ga Farfesa Ango Abdullahi.

Ya yi magana ne a kan abun da ya je ya dawo kan sanarwar da ya fitar bayan NEF ta amince da ‘yan takarar yarjejeniya na jam’iyyar PDP.

Ya ce sanarwar ta samu amincewa da albarkar shugabansu Farfesa Ango Abdullahi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Babu baraka a kungiyar dattawan arewa, muna biyayya ga Ango Abdullahi – Baba Ahmed
Babu baraka a kungiyar dattawan arewa, muna biyayya ga Ango Abdullahi – Baba Ahmed Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Da yake jawabi a wajen wani taro da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya a jihar Kaduna a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, Baba-Ahmed ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya nakalto Baba-Ahmed yana fadin:

“Ban aikata abu sabanin na shugabanmu wanda muke mutuntawa sosai ba. Da farko jawabin da na saki jawabinsa ne. Bani da ikon sakin wani jawabi.
“Muna biyayya gare shi. Abun da ya aikata kan yarjejeniya abu ne mai kyau. Abun da ya so aikatawa a bayyane yake. Ya aikata abun da ya aikata a matsayin Farfesa Ango Abdullahi ba wai a matsayin jagora ko shugaban kungiyar dattawan arewa ba.
“Amma bama adawa da shi. Dan Najeriya ne da ake mutuntawa sosai. Jajirtacce ne shi wajen ganin shugabanci nagari. Muna biyayya gare shi.
“Ba a taba samun baraka a kungiyar dattawan arewa ba kuma ba za a taba samu ba. Shugabanmu shine Farfesa Ango Abdullahi. Ana mutunta shi.”

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Da yake ci gaba da jawabi, ya bayyana cewa:

“Abun da ya faru a kasar nan a shekaru da suka gabata, mun zabi gurbatattun shugabanni. Ina ganin ba laifinsu bane face laifinmu muna.
“Wani abu na damunmu a matsayinmu na kasa, bama zabar shugabanni nagari wadanda suka damu da kasar maimakon haka muna zabar shugabanni wadanda suka damu da kansu.
“Ya zama dokle yan Najeriya su yi takatsantsan imma mu zabi shugabanni nagari a 2023 ko kuma wadanda za su zo su fiye na yanzu muni.”

An yanka ta tashi a PDP bayan Dattawan Arewa sun ce ba su tsaida Bala da Saraki ba

A baya mun ji cewa kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, ta nesanta kanta daga rahoton da ke cewa ta zabi Bala Mohammed da Bukola Saraki da su rike tutar PDP daga Arewa.

Daily Trust ce ta rahoto kungiyar nan ta NEF ta bakin darektanta na yada labarai da wayar da kan al’umma, Hakeem Baba-Ahmed, ya na karin haske a kan maganar.

Kara karanta wannan

An yanka ta tashi a PDP bayan Dattawan Arewa sun ce ba su tsaida Bala da Saraki ba

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa masu neman takara a PDP ne suka kawo maganar a fito da ‘dan takara guda daga Arewa a cikinsu ta hanyar yin maslaha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel