An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

  • Gwamna Kayode Fayemi ya hadu da Rotimi Akeredolu saboda maganar yin takara a zaben 2023
  • Dr. Fayemi yana tunanin tsayawa neman kujerar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC
  • Zuwa yanzu bai tsaida magana ba, amma gwamnan ya ce irinsa al’ummar kasar nan suke bukata

Ondo - A lokacin da ake shirin gudanar da zaben fitar da gwani, sai aka ji gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi yana maganar shiga takara a zaben 2023.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto da cewa Dr. Kayode Fayemi ya ziyarci abokin aikinsa, Rotimi Akeredolu a kan batun yin takarar shugaban kasa a APC.

Gwamna Kayode Fayemi ya zanta da ‘yan jarida bayan ya zauna da gwamnan jihar Ondo, ya ce har yanzu bai yanke shawara a kan matakin da zai dauka ba.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Dr. Fayemi ya ce har zuwa ranar Talatar nan kenan, yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki ne a APC. Gwamnan ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter.

Tsohon Ministan tarayyar ya bayyana kan shi a matsayin wanda ya dade yana gwagwarmaya a siyasar Najeriya tun a matakin siyasar dalibai a jami’a.

Baya ga haka, Fayemi ya ce sun kafa kungiyoyi masu zaman kansu, daga bisani ya rike kujerar gwamna, Minista har ya zama shugaban duka gwamnoni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Ekiti
Gwamna Fayemi da Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Na san ciwon kan Najeriya - Fayemi

“Na yarda cewa ina da abin da ake bukata wajen fahimtar matsalar kasar nan da wahalar sha’aninta wajen shawo kan kalubalen da ake fuskanta.”

- Kayode Fayemi

Gwamnan na jihar Ekiti ya ce zai iya kawo sababbin dabaru na yarda za a ciyar da kasar nan gaba idan ya samu takara a jam’iyyar APC, ya kai ga samun mulki.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Kasarmu ta samu muhimman cigaba, an ci nasarori a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, amma ba a kammala aikin ba, akwai abubuwan da suka rage.

“Najeriya ta na bukatar wanda ya kware, yake da ilmi, ya san kan aiki, musamman maras tsoro.” - Kayode Fayemi

Gwamnan ya ce zai hada kan ‘yan Najeriya idan ya samu dama, don haka ya ziyarci Akeredolu da mutanen jihar Ondo wanda ‘yanuwan mutanen jihar Ekiti ne.

Abiodun yana tare da Osinbajo

Zaben wanda zai marawa baya ya zama ‘dan takarar APC ya sa kan Gwamna Dapo Abiodun ya rabu biyu tun da Bola Tinubu da Yemi Osinbajo su na takara.

Mataimakin shugaban kasa ya fito takara kuma asalinsa mutumin Ogun ne, sannan Bola Tinubu yana neman mulki a APC, hakan ya raba kan wasu 'yan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel