Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa

Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa

  • Matasa sun yiwa wani dan majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Oluwole Ogunmolasuyi, ihu tare da fatattakarsa daga mazabarsa
  • An tattaro cewa sun aikata masa hakan ne saboda rashin yi masu aiki tare da watsar da su tun bayan da suka zabe shi
  • Sai dai, dan majalisar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wani abokin hamayyarsa ne ya kwaso yan daba don su aikata masa haka

Ondo - Wani dan majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Oluwole Ogunmolasuyi, ya gamu da fushin al’ummar mazabarsa inda suka kai masa farmaki kan zargin rashin yi masu aiki.

Ogunmolasuyi ya kasance dan majalisa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltan mazabar Owo 1 kuma shine shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin na jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An ji muryar wani dan majalisar tarayya na PDP na barazanar kashe wani

Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa
Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa Hoto: Punch
Asali: UGC

Wani mai amfani da shafin Facebook, Tosin Fapohunda II, ne ya wallafa bidiyo wanda a ciki ne aka farmaki dan majalisar.

Ya rubuta:

“Matasan mazabar wani dan majalisar jihar Ondo sun fatattake shi kamar barawo da rana tsaka a yau kan rashin yi masu aiki da kuma kauracewa mazabarsa tun bayan da aka zabe shi domin ya wakilce su a majalisar dokokin jihar Ondo.
“Matasa sun fatattaki shugaban masu rinjaye a majalisar jihar Ondo Honourable Ogunmolasuyi wanda aka fi sani da West daga mahaifarsa yayin da ake rade-radin sake daura masu shi da kuma rashin yin abun kwarai.”

A cikin bidiyon, saura kadan fusatattun matasan wadanda suka dauki sanduna da duwatsu su lallasa Ogunmolasuyi, suna masu cewa “Allah ya kwashe maka West. Muna kalubalantarka idan ka isa ka sake zuwa nan.”

Kara karanta wannan

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

Ga bidiyon a kasa:

Dan majalisar ya yi martani

Jaridar Punch ta rahoto cewa dan majalisar ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce lamarin ya afku ne a ranar Lahadi da ta gabata.

Ya ce:

“Muna da gudunma biyar a mazabata kuma daya daga cikinsu shine Iloro kuma ni na fito ne daga Igboroko, don haka wannan gudunmar ba tawa bace, amma tana daya daga cikin gudunmar da ke karkashin mazabata.
“Akwai dan takara daga wannan gudunmar da ke neman kujerar a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP. An fada mani cewa shine ya tara yan iska zuwa wajen, amma na riga na wuce.
“Na kalli bidiyon sau da dama, wadannan matasan da na gani ba mutane ne da za su wakilci mutanen arziki na Owo ba. Owo na da manyan mutane da dama, musamman ma a Iloro; suna da manyan mutane da yawa. Idan basa son wani wakili, ya ka mata su samu wayayyiyar hanyar tunkararsa. Wadannan mutanen da na gani ba mutane ne da za su iya cima al’ummata ko mazabata albasa ba.”

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu da ihun 'Ba ma yi' bayan ya ziyarci mazabarsa

A wani labari makamancin wannan, Hon. Musa Suleiman Nasko, dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Magama ta jihar Neja ya sha da kyar a hannun al’umman mazabarsa.

A wani bidiyo da shafin the_northern_trend_blog ya wallafa a Instagram, an gano yadda mutanen mazabarsa suka dunga jifarsa da duwatsu.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne bayan dan majalisar ya ziyarci mazabar tasa domin jajantawa mutanen garin Magama wadanda rikicin ‘yan fashin ya cika da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel