Da Dumi-Dumi: Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya

Da Dumi-Dumi: Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya umarci a kama ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo ko ina ya shiga
  • Wike ya dauki wannan matakin ne bisa zargin ɗan majalisar ya tura yan daba Sakariyar PDP dake Patakwal su ta da yamutsi
  • Sai dai bayanai daga bnagaren wanda ake zargin sun nuna cewa ba shi da masaniyar duk abinda ya faru

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana neman mamba a majalisar wakilan tarayya kuma ɗan takarar gwamna, Farah Dagogo, ruwa a jallo, duk inda aka ganshi a cafke shi.

The Nation ta rahoto cewa Wike ya ɗauki wannan matakin ne bisa zargin ya ɗauki hayar yan ƙungiyar asiri sun farmaki Sakatariyar PDP dake Patakwal.

Gwamnan, a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin Midiya, Kelvin Ebiri, ya fitar, ya umarci rundunar yan sandan Ribas ta damƙe Dagogo.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Janar Idris Dambazau ya gudu daga hannun hukumar rashawa a Kano

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Da Dumi-Dumi: Gwamna Wike ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo kan abu ɗaya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wike ya zargi ɗan majalisar tarayyan da ɗakko hayar yan daban kungiyar asiri, waɗan da suka mamaye Sakatariyar PDP a Patakwal, suka kawo cikas a aikin tantance yan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sanarwan Wike ya ce:

"Cikin gaggawa yan sanda su kama Farah Dagogo a duk inda ya shiga, kuma wajibi ne a hukunta shi. Tuni wasu daga cikin yan daban da ya ɗakko suka shiga hannu, kuma zamu tabbatar doka ta yi aiki a kan su."

Shin dagaske shi ya ɗakko yan daban?

Sai dai wata majiya daga cikin makusantan ɗan majalisan ta ce Dagogo bai san komai ba game da abin da ya auku a Sakatariyar PDP.

Ya ƙara da bayanin cewa wasu tawagar yan takara ne dake hangen kujerun majalisar jiha da na ƙasa ne suka yi zanga-zangar nuna fushinsu saboda kwamiti ya ƙi tantance su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

Ya ce:

"Suna cikin zanta wa da yan jarida a wurin, yan sanda suka ƙariso suka fara harbin iska. Sun kame wasu yan takara sun tafi da su, Dagogo baya wurin, dan me za'a ayyana nemansa?"

A wani labarin kuma Ana raɗe-raɗin sauya sheka, mataimakin gwamna da Kwamishinoni 10 sun yi murabus

Yayin da ake yaɗa jita-jitar sauya shekar Tambuwal bayan ya gana da Buhari, kwamishinoninsa 11 sun aje aikinsu.

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Ɗan'iya, ya sauka da kujerar kwamishinan kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel