Matashin ‘Dan siyasa ya shiga NNPP, watakila ya yaki Kwankwaso wajen samun takara

Matashin ‘Dan siyasa ya shiga NNPP, watakila ya yaki Kwankwaso wajen samun takara

  • Jam’iyyar hamayyar nan NNPP ta samu karin magoya baya a sakamakon shigowar Olufemi Ajadi
  • Kwamred Olufemi Ajadi wanda yana harin kujerar shugaban kasa ya yi rajista da jam’iyyar NNPP
  • Matashin ya bayyana cewa manufofin NNPP ne suka dace da shi saboda ya ga za a tafi da matasa

Abuja - Daya daga cikin masu harin shugabancin Najeriya, Olufemi Ajadi ya shiga jam’iyyar nan ta NNPP wanda ake yi wa take da mai kayan marmari.

Jaridar Vanguard ta ce Kwamred Olufemi Ajadi ya yi rajista da jam’iyyar adawa ta NNPP bayan ya gama shawarwari da tattaunawa da yake yi da jama’a.

A ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu 2022 aka ga Olufemi Ajadi tare da manyan shugabanni da jagororin NNPP a sakatariyarta a birnin tarayya Abuja.

Wadanda suka yi wa Ajadi rakiya zuwa babbar sakatariyar jam’iyyar sun hada da ‘ya ‘yan NNPP na reshen jihohin Legas da Ogun da wasu magoya baya.

Kara karanta wannan

An buga an bar ka: Abin da ya sa aka gagara tsige ni daga shugaban majalisar - Bukola Saraki

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ya zama cikakken ‘dan jam’iyya mai kayan marmari, Ajadi ya yi bayanin abin da ya sa ya dauki wannan matakin.

Ajadi ya kama hanyar kawo gyara

Kwamred Ajadi ya ce yana daf da cin ma burinsa na kawo gyara ta hanyar rike kujerar siyasa.

Jagororin NNPP
Oluwafemi Ajadi da mutanensa tare da Rabiu Kwankwaso Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Matashin yake cewa ya zabi ya rungumi NNPP ne bayan ya yi ta tattaunawa da mutane. A karshe ya fahimci jam’iyyar ce ta fi dacewa da burinsa a siyasa.

“Wannan jam’iyya ce da ta ke da manufofi da ya yi kama da gwagwarmyar da mu ke yi tun tuni.”
“Jam’iyya ce wanda na yi imanin tayi wa dinbin matasan Najeriya tanadi, wanda kuma ni ina cikin masu wakiltarsu, da kuma sauran mutanen Najeriya.”
“Saboda haka ina kira ga matasan kasar nan su shirya. Lokaci ya yi da za mu kawo canjin da mu ka dade mu na fata.”

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Zai nemi tikitin shugaban kasa?

Daga sakatariyar NNPP, sai Ajadi ya kai gaisuwa ga jigon jam’iyya, Rabiu Musa Kwankwaso. An ji Kwankwaso yana cewa zaben 2023 zai zo da sauye-sauye.

Kawo yanzu Ajadi bai bayyana matsayarsa a kan batun takarar shugaban kasa ba, amma ya nuna zai yi kokari wajen jawowa jam’iyyar karin magoya baya.

Kwanaki ku ja ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso, ya sauya-sheka zuwa NNPP, kuma har ya bukaci matasa su shiga jam'iyyar adawar.

Idan har matashin ya zabi ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin NNPP, zai gwabza da sabon jagoran jam’iyyar na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng