Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

  • Hukumar NDLEA ta mika wasika ga shugabannin jam'iyyar APC, ta ce ya kamata a yiwa 'yan takara gwajin kwaya
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da APC ke shirin gudanar da zaben fidda gwani gabanin babban zaben 2023
  • Hukumar ta NDLEA ta bayyana dalilinta na fadin haka, ta ce hakan zai fa'idanci 'yan Najeriya matuka gaya

Shugaban hukumar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa (rtd) ya rubuta wasika ga shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu, inda ya bukaci a baiwa jami’an NDLEA damar gudanar da gwajin tabbacin kubuta daga shan kwaya ga 'yan siyasa da ke neman takara.

Marwa ya ce a lokacin da PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zabukan fidda gwani, zai kuma rubuta musu wannan bukata ta gwajin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Dan Jam’iyya ya rubutawa Shugabannin APC takarda, yana so a hana Gwamna tazarce

Akwai bukatar a yiwa 'yan siyasa gwajin shan kwaya
Babbar magana: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasa gwajin shan miyagun kwayoyi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban na NDLEA wanda ya ke jawabi a wajen bikin karramawar kwata-kwata na farko a 2022 na hukumar a Abuja ya bayyana cewa gwajin shan kwaya ya zama dole don tabbatarwa da samar da ‘yan siyasa masu muhimmanci a ofisoshin gwamnatin kasar nan.

Ya bayyana cewa, dabarar hakan shi ne a dakile 'yan siyasa daga amfani da kason kasafin kudi wajen sayen hodar iblis ko maganin Methamphetamine maimakon samar da ayyukan da suka cancanta ga talakawa.

Da yake karin bayani, gidan talabijin na Channels ya ruwaito Marwa na cewa:

“Ba wai ‘yan siyasa kadai ba, har da wadanda gwamnati ta nada, kuma da safiyar yau na aika wasika zuwa ga Shugaban jam’iyyar APC na kasa, wanda zai kasance na farko a cikin kwamitin ayyuka na kasa da nake son kai wa ziyarar neman shawara kan wannan batu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

"Na ba da shawarar cewa a shigar da gwaje-gwajen miyagun kwayoyi a cikin tsarin tantancewa ga duk wadanda ke sha'awar tsayawa takarar mukaman gwamnati; Haka kuma za mu yi wa PDP da sauran muhimman jam’iyyu.”

‘Dan Jam’iyya ya rubutawa Shugabannin APC takarda, yana so a hana Gwamna tazarce

A wani labarin, Ayodele Oludiran wanda yana cikin ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ogun, ya kai karar gwamnansa wajen shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu.

Daily Trust ta ce Ayodele Oludiran ya gabatar da korafinsa gaban Sanata Abdullahi Adamu, yana mai jan kunnensa a kan sake ba Gwamna Dapo Abiodun takara.

Rahoton ya tabbatar da cewa takardar korafin ‘dan jam’iyyar ta shiga sakatariyar APC na reshen jihar Ogun da ke garin Abeokuta ranar 12 ga watan Afrilu 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel