Shirin 2023: Yahaya Bello ya gana da Buhari domin nuna masa fom din takarar shugaban kasa

Shirin 2023: Yahaya Bello ya gana da Buhari domin nuna masa fom din takarar shugaban kasa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin dan takarar da ke son gaje kujerarsa a zaben 2023
  • Shugaban ya karbi gwamna Yahaya Bello ne a fadarsa domin ganin fom din takarar shugaban kasa da ya saya
  • 'Ya'yan jam'iyyar APC na ci gaba sayen foma-foman takarar shugaban kasa na zaben 2023 mai zuwa nan kusa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a fadarsa da ke Aso Rock Villa da ke Abuja.

Ganawar tasu ta zo ne daidai lokacin da gwamnan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki gabanin zaben fidda gwani.

Ganawar Buhari da Yahaya Bello gabanin zaben 2023
Shirin 2023: Yahaya Bello ya gana da Buhari domin nuna masa fom din takarar shugaban kasa | Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Fadar shugaban kasa ta ce, gwamnan ya gana da Buhari a yau Alhamis 28 ga watan Afrilu, kamar yadda hadimin shugaba Buhari ya yada wasu hotunan shugaban da gwamnan ta shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

Sanarwar da Buhari Sallau ya yada ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi H.E. Yahaya Bello a fadar gwamnati ranar 28 ga Afrilu 2022."

Legit.ng Hausa ta yi duba ga hotunan, inda ta ga shugaban kasar tare da gwamnan sun dauki hoto rike da fom din nuna sha'awar tsayawa takara na jam'iyyar APC.

Wannan ke nuni da cewa, gwamnan ya kai shugaba Buhari fom din ne watakila tare da neman goyon bayansa na kudurin mulkar Najeriya a zaben 2023.

Shugaban kasa Muhammadu ya sha karbar 'yan siyasar Najeriya; musamman daga APC da ke da sha'awar gaje kujerarsa, inda suke neman shawari da goyon bayansa kafin su ci gaba da fafuka.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Kara karanta wannan

Bayan ya sa labule da Buhari: Ana rade-radin Tambuwal zai sauya sheka daga PDP zuwa APC

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel