Rochas Okorocha da wasu Sanatoci 3 da za su yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Rochas Okorocha da wasu Sanatoci 3 da za su yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023

  • Ana kyautata zaton wanda zai rikewa APC tuta a zaben shugaban kasan 2023 zai fito ne daga kudu
  • Hakan ta sa aka samu wasu ‘Yan majalisa daga kudancin Najeriya da suke shirin tsayawa takara
  • Wadannan Sanatoci sun yi fice a siyasa, kuma an yi shekaru ana gwabzawa da dukkaninsu a siyasa

Abuja - A rahoton na mu na yau, mun tattaro sunayan ‘yan majalisar dattawan da aka san su na da shirin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Jerin yana dauke da Sanatoci da suke a kan mulki a yau. Baya ga wadannan akwai wasu tsofaffin Sanatocin da za su shiga neman takarar shugaban kasar.

A cikin wadanda suka taba rike kujerar Sanata da suke harin shugabancin Najeriya a 2023 akwai Anyim Pius Anyim, Bukola Saraki da Asiwaju Bola Tinubu.

Haka zalika akwai irinsu Rabiu Musa Kwankwaso wanda zai yi takara a karkashin jam’iyyar NNPP.

Jerin Sanatocin

1. Rochas Okorocha

Sanatan Imo ta yamma a majalisar dattawa, Rochas Okorocha yana sha’awar fitowa takarar shugaban kasa a APC a zaben da za a shirya kwanan nan.

Ba wannan ne karon farko da tsohon gwamnan na jihar Imo ya nemi tikitin yin takarar shugaban kasa ba. Okorocha yana sa ran ya kai labari a zaben 2023.

Majalisa
Zaman majalisar dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

2. Orji Uzor Kalu

A jerin na mu akwai Sanata Orji Uzor Kalu wanda yanzu haka shi ne mai wakiltar mutanen Arewacin jihar Abia a majalisar dattawa a karkashin APC.

Shi ma Orji Uzor Kalu tsohon gwamna ne a Abia, kuma ya taba yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PPA, a lokacin Ummaru ‘Yar’adua ya lashe zabe.

3. Ibinkunle Amosun

A ranar Larabar nan aka ji labari Ibinkunle Amosun zai nemi takarar Shugaban kasa. Sanatan na Ogun ta tsakiya shi ne na karshe da ya ayyana burinsa a APC.

Kamar sauran abokan aikinsa, Amosun ya yi shekaru takwas yana gwamna a Ogun. Sanatan ya ce idan ya karbi shugabancin Najeriya, zai kai kasar ga ci.

Na san sirrin gwamnati - Osinbajo

Kwanaki aka rahoto Yemi Osinbajo ya na cewa da Buhari ya je ganin Likita a kasar waje, ya gano wasu abubuwan da babu wani wanda ya san da su a gwamnati.

Farfesa Osinbajo ya ce ya san Ubangiji ke bada mulki, amma yana ganin babu adalci a ce ya bar Aso Villa ya koma kauyensa ba tare da ya yi takara a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel