Siyasar Najeriya
Wata babbar kotun jihar Gombe ta bayar da belin Bala Sani mai shekaru 47, wani dan kasuwa mazaunin Abuja da aka tsare bayan ya caccakar gwamnatin Gwamna Yahaya.
Shehu Sani ya ce wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar PDP.
A daren yau ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gana da Mallam Mamman Daura, dan uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma shugaban mukarraban Aso Rock.
Ɗan takarar mataimakin Gwamna a jam’iyyar APC Alhaji Murtala Sule Garo ya musanta rahoton cewa ya fice daga jam’iyyarsu ta APC zuwa PDP ko NNPP mai kayan dadi.
Wasu a APC su na kukan ana yunkurin ba Goodluck Jonathan tikitin APC, suka ce Ba zai yiwu a tsaida masa Dr. Jonathan takara a zaben 2023 bayan kifar da PDP ba.
Amb. Aminu Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo su na rikici da Shehu Wada Sagagi a kan shugabancin PDP. Wannan rigima ta jawo kowane bangare sun yi zabensu dabam
Tsohon Ministan ilmi ya ce har da doya aka saida domin ya tsaya takara a APC. Mutane 3100 su ka ba Chukwuemeka Nwajiuba gudumuwa, a ciki har da wani manomi.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama Sanata Rochas Okorocha a gidansa ta tafi dashi bayan kai ruwa rana a gidan nasa.
WanI ya rasa ransa a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ya gudana a karamar hukumar Billiri da ke jihar Gombe a ran Lahadi.
Siyasar Najeriya
Samu kari