Ba abin kunya bane na nemi a mayar min da kudin fom: Dan Namadi Sambo ya magantu kan shan kaye a zaben PDP
- Adam Namadi Sambo, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya tabbatar da cewar yaba deleget kudi domin samun kuri’unsu
- An tattaro cewa Sambo wanda ya samu kuri’u biyu a zaben fidda gwanin PDP ya baiwa deleget din naira miliyan biyu kowannensu don su zabe shi
- Sai dai kuma ya ce bai aikata abun kunya ba don ya nemi a dawo masa da kudinsa domin tun farko manyan masu ruwa da tsaki sun nemi a mayarwa wadanda suka fadi kudadensu
Kaduna - Adam Namadi Sambo, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya ce babu wani abun kunya don ya nemi delegate su dawo da kudaden da ya raba masu bayan ya fadi zaben fidda gwani, Daily Trust ta rahoto.
Sambo dai ya rasa samun tikitin dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kaduna ta arewa a karkashin PDP.
Mun dai ji yadda Adam da wani dan takarar, Shehu Usman ABG suka nemi a dawo masu da miliyoyin naira da suka baiwa deleget bayan sun sha kaye a hannun dan majalisa mai ci, Samaila Suleiman wanda a kwanan nan ne ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
An rahoto cewa Suleiman ya raba tsakanin naira miliyan 3.5 da 4 don saye deleget a bangarensa, hakan ya sa shi yin nasara kan Usman Shehu ABG da kuri’u 20.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi zargin cewa ABG ya rabawa deleget naira miliyan 2.5 kuma ya samu kuri’u 14 yayin da Sambo wanda ya raba masu naira miliyan 2 kowannensu ya samu kuri’u biyu.
Sai dai, Adam Sambo a wata sanarwa da ya aikewa Daily Trust a yau Laraba, ya tabbatar da cewar ya nemi a dawo masa da kudinsa, sai dai ya ce baya aikata haka a killace kamar yadda sauran na suka aikata haka.
Sambo ya ce da farko masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun bukaci dukka deleget din da su dawo da dukka kudaden da yan takarar da suka sha kaye suka basu.
Jawabin ya ce:
“An ja hankalina zuwa ga wata wallafa da Daily Trust ta yi a shafinta na yanar gizo mai taken ‘Dirama yayin da dan Namadi Sambo ya nemi deleget su dawo masa da kudinsa bayan ya gaza samun tikitin PDP.’
“Ina burin bayyana cewa a zahirin gaskiya, babu wani dirama game da bukatar, kuma abun takaici ne kafofin watsa labarai sun yada shi a matsayin haka. Deleget da kansu suna da sane da umurnin da manyan masu ruwa da tsaki na PDP a mazabar Kaduna ta arewa suka bayar, cewa su mayar da duk kudaden da yan takarar da basu yi nasara ba suka basu na neman goyon bayansu a zaben fidda gwanin.
“An yi hakan ne don karfafawa deleget gwiwar zabar yan takara bisa la’akari da cancantarsu ba wai karfin kashe kudinsu ba, kuma don kama su kan yan takarar da suka zaba.”
Dan tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ce domin mutunta wannan yarjejeniyar, wasu deleget a mazabar Kaduna ta arewa sun fara neman yan takarar da basu yi nasara ba a zaben majalisar jiha wadanda aka gudanar da zabensu kafin nasu, “wanda na abokin takarata Shehu Usman ABG dani ya biyo baya. kuma ni. Saboda haka, ban aikata haka a ware ba ko kuma yin abun dariya ba.”
Ya ce ya dauki lamarin da zuciya daya kuma zai ci gaba da marawa PDP baya tare da yin iya bakin kokarinsa don kare nasararta.
Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani
A wani labarin, tsohon dan majalisa daga jihar Kaduna, Datti Ahmed, a ranar Talata ya bayyana janyewarsa daga takarar gwamnan jihar Kaduna.
Bayan haka kuma, wani dan takaran, Shehu Sani, ya ce yana ci gaba da fafutukarsa ta fitowa takarar gwamna a jam’iyyar PDP.
'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP
Sani, wanda tsohon Sanata ne, ya kuma sha alwashin cewa ba zai baiwa deliget cin hancin da za su zabe shi ba.
Asali: Legit.ng