Shirin 2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

Shirin 2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

  • Rahoton da muke samu daga jihar Zamfara yua bayyana cewa, dan takarar gwamna na PDP kuma tsohon mataimakin gwamna ya janye daga takara
  • Wannan na zuwa ne daidai loakcin da jam'iyyar ke ci gaba da zaben fidda fidda gwani gabain babban zaben 2023 mai zuwa
  • Mahdi Aliyu Gusau, shi ne tsigaggen mataimakin gwamnan Zamfara bayan samun sabani da gwamnan jihar; Muhammad Bello Matawalle

Gusau, Zamfara - Gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fice daga takarar.

Channels Tv ta rahoto cewa, Mahdi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarensa Umar Aminu a Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗan takarar gwamna a PDP ya janye daga zaɓen fidda gwani, ya fara shirin komawa APC

Mahadi Aliyu Gusau ya janye daga takara
Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mahdi Gusau ya bukaci deliget-deliget, shugabannin jam’iyyar, da magoya bayansa da su zabi Dr. Lawal Dauda ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar ta Zamfara.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana dalilinsa na ficewa daga takarar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba Mahdi kadai aka samu daga PDP cikin wadanda suka janye daga takarar gwamna ba, Channels Tv ta ruwaito cewa, dan takarar gwamnan jihar Abia na PDP, Sanata Abaribe shi ma ya janye daga takara.

Idan baku manta ba, rahotannin Legit.ng Hausa a baya sun kawo yadda aka tsige Barista Mahdi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara a watan Fabrairun wannan shekara bayan sauya shekar mai gidansa daga PDP zuwa APC.

Shehu Sani: Dan takarar PDP ya kwato N100m daga hannun deleget ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar da zai gaji Buhari

A wani labarin na daban, wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin toshiyar baki gabannin zaben fidda dan takarar jam’iyyar.

Tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani ne ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Talata, 24 ga watan Mayu.

Sani ya bayyana cewa dan takarar ya kwato kudin ne bayan ya gaza samun tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi, kuma ya yi amfani da 'yan banga da mafarauta ne wajen karbo kudin nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel